logo

HAUSA

Burin ’yan siyasan yammacin duniya shi ne, halaka sana’ar auduga ta jihar Xinjiang domin haddasa tashe-tashen hankula a cikin kasar Sin

2021-03-27 17:07:40 CRI

Burin ’yan siyasan yammacin duniya shi ne, halaka sana’ar auduga ta jihar Xinjiang domin haddasa tashe-tashen hankula a cikin kasar Sin_fororder_hoto

Jiya Jumma’a, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar kakabawa mutane 9 da kamfanoni 4 na kasar Burtaniya takunkumi domin mai da martani kan takunkumin da kasar ta kakabawa wasu kamfanoni da daidaikun mutanen Sin, bisa hujjar batun hakkin dan Adama na jihar Xinjiang ta kasar Sin. Kasar Sin ba za ta yi hakuri ko kadan ba kan wadanda suke neman bata ci gaban jihar Xinjiang da kuma tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar ba.

Cikin ’yan kwanakin nan, masu adawa da gwamnatin kasar Sin dake yammacin duniya suna ci gaba da yada jita-jita cewa, wai “ana tilastawa al’ummomin jihar Xinjing shuka auduga”.

Amma, bisa bayanin da hukumar kula da harkokin gona ta jihar Xinjiang ta fidda, ana gudanar da kashi 69.83 bisa dari na aikin tsinkar auduga da na’urori a duk fadin jihar Xinjiang, har ma wannan adadin ya kai 95% a arewacin jihar. Mutanen jihar Xinjiang sun gabatar da hotuna da bidiyo da dama game da yadda suke gudanar da aikin tsinkar auduga. Cikin hotunansu, an ga yadda motar tsinkar auduga take aiki a gonar auduga, ba tare da mutane a cikin gonar ba.

Ban da haka kuma, aikin tsinkar auduga ya zama aikin dake iya samar da kudin shiga masu yawa ga mutanen jihar Xinjiang, har wasu mutane na sauran sassan kasar Sin su kan tafi jihar Xinjiang domin gudanar da wannan aiki. A lokacin tsinkar auduga kimanin kwanaki 50 a kowace shekara, kowane ma’aikacin dake tsinkar auduga zai iya samun albashin yuan sama da dubu 10 (kwatankwacin dalar Amurka 1550 ko fiye), shi ya sa, babu bukatar a tilastawa wani ko wata yin wannan aiki.

Shi ya sa, al’ummomin jihar Xinjiang suka fusata matuka dangane da jita-jitar da masu adawa da kasar Sin suka yada, Migit Timit mai sana’ar auduga a jihar Xinjiang ya bayyana cewa, suna yada jita-jita domin hana sayen auduga daga wajenmu, lamarin da zai sa mutanen jiharmu kasa samun aikin yi, da kuma sake shiga yanayin kangin talauci, ba za mu yarda ba!

Maganar Migit Timit ta tona mugun kulli na ’yan siyasar yammacin duniya.

A bangare guda, suna neman bata sunan jihar Xinjiang da na kasar Sin, domin kakkabawa kasar Sin takunkumi. A daya bangaren kuma, suna son lalata sana’ar auduga ta jihar Xinjiang baki daya, domin wannan sana’a ta zama babbar sana’ar dake tabbatar da ci gaban tattalin arziki a jihar Xinjiang. In sun cimma mugun kullinsu na hallaka sana’ar baki daya, za a haddasa tashe-tashen hankula a jihar Xinjiang, lamarin da zai hana bunkasuwar kasar Sin.

Amma, kasar Sin tana da kasuwanni masu dimbin yawa a cikin gida, kuma akwai kasuwanni da dama cikin kasa da kasa, ba za a tsayar da bunkasuwar sana’ar auduga a jihar Xinjiang ba, domin takunkumin da wasu kasashen yammacin duniya suka sanyawa kasar Sin. Sana’ar auduga babbar sana’a ce dake samar da wadata ga al’ummomin jihar Xinjiang, tabbas, gwamnatin kasar Sin za ta dukufa wajen inganta wannan sana’a domin kare al’ummomin jihar Xinjiang. Idan ’yan siyasar yammacin duniya suka ci gaba da yada jita-jita game da jihar Xinjiang, tabbas, Sin za ta mayar musu da martani. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)