logo

HAUSA

Akwai bukatar hada kai domin kiyaye muhallin duniyarmu

2021-03-27 15:30:57 CRI

Akwai bukatar hada kai domin kiyaye muhallin duniyarmu_fororder_环保

Yau ranar 27 ga watan Maris, rana ce da asusun kiyaye halittun duniya wato WWF ya kebe domin dakile sauyin yanayi ta hanyar tsimin makamashi, inda ya gabatar da shawarar cewa, a ranar Asabar ta karshe a watan Maris na kowace shekara, a kashe wutar lantarkin fitilu da na’urorin da ba dole a yi amfani da su ba, har tsawon awa guda daya wato tsakanin karfe takwas da rabi zuwa tara da rabi na dare, domin nuna goyon baya ga aikin dakile sauyin yanayin da ake kokarin gudanarwa a fadin duniya. Ana kiran aikin da sunan “awa daya ta duniya” ko “awa daya ta kashe wutar lantarki”.

Sauyin yanayi, kalubale ne ga daukacin bil Adama, kuma kalubale ne dake tunkarar duk duniya, ya dace al’ummar kasashen duniya su hada kai, kuma su gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninsu, domin dakile matsalar tare, haka kuma akwai bukatar kiyaye muhalli ta hanyar tsimin makamashi, shi ya sa ana iya cewa, matakin da kungiyar WWF ta dauka na kebe ranar kashe wutar lantarki a fadin duniya, yana da babbar ma’ana.

Bisa matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, a ko da yaushe kasar Sin tana kokari matuka domin sauke nauyin da ya dace da matakin ci gabanta da yanayin da take ciki dake wuyanta wajen dakile matsalar sauyin yanayi, ta hanyar daukar hakikanin matakai.

Reshen kungiyar WWF da aka kafa a kasar Sin ta taba gabatar da shawarwari da dama a shekarar 2018 ga al’ummun kasar domin su sauya wasu hanyoyin rayuwarsu, wadanda ke kunshe da rage ledar da ake amfani da ita a yau da kullum, da sayen kayayyakin dake da alamar kiyaye muhalli, da yin odar abincin da ya dace a dakin cin abinci domin kaucewa barnatar da abinci, da kin sayen kayayyakin da aka samar da namun daji, da rage kayayyakin da ake amfani da su sau daya kawai, da zabar hanyoyin sufuri marasa gurbata muhalli, da rarrabawa da kuma sarrafa bola ta hanyar da ta dace, da juya bolar kayayyakin laturoni, da dai sauransu, ta yadda za a kare doron duniyarmu daga hadduran muhalli.

Daga matakan shawo kan gurbatar iska, da ruwa, da kuma kasa da gwamnatin kasar Sin ta dauka, an lura cewa, tana mai da hankali sosai kan aikin kiyaye muhalli, nan gaba kuma za ta ci gaba da cudanya tsakaninta da sauran kasashen duniya, yayin da suke kokarin dakile matsalar sauyin yanayi, kuma kasar Sin tana son yin kokari tare da su, domin tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar Paris, wadda aka daddale domin tunkarar matsalar sauyin yanayi, tare kuma da ingiza dauwamammen ci gaban tattalin arziki a fadin duniya ba tare da gurbata muhalli ba.

A nasa bangaren, babban sakataren MDD Antonio Guterres shi ma ya gabatar da wani jawabi ta kafar bidiyo a shafin yanar gizon Microblog na majalisar a yau, inda ya jaddada cewa, shekarar bana ta 2021, shekara ce da duniya za ta yi manyan sauye-sauye, a don haka wajibi ne kowanenmu ya ba da gudummowarsa domin kare duniyarmu, saboda karamin aiki zai kawo babban tasiri, kuma ya kira al’ummomin sassa daban daban a fadin duniya su shiga aikin nan mai ma’ana, ta yadda za su sanar da anniyarsu ta kare duniyar bil Adama ga kowa da kowa. (Jamila)