Tabbatar da samun kuzari a kullum a gundumar tsaunukan Qinling
2021-03-26 16:07:32 CRI
Yanzu haka rana ke fitowa a tsaunikan Qinling, kuma agogo na cewa 6:30. Dattijo Peng Lizhu mai shekaru 75 da haihuwa, ya fara da wasan kwallon tebur na “pingpong” tare da abokan sa a cibiyar wasanni dake gundumar Shanyang dake lardin Shaanxi na kasar Sin.
Peng daya ne daga mutane sama da 100 dake motsa jiki duk safiya, a dakin wasanni dake wannan lardi. Da yake tsokaci game da hakan, Peng ya ce "Kayan wasa dake wannan filin wasa na da kyau. A kullum ina wasan kwallon tebur har tsawon sa’oi 2. Wasu kuma suna wasan badminton, wasu suna gudu, wasu kuma na yin wasan tai chi,".
Ya ce "A yanzu akwai kayan wasa masu inganci, mutane da yawa na son kasancewa cikin koshin lafiya. Karin lafiya na sa mu karin jin dadi."
Motsa jiki ya zama wani sabon salon rayuwa ga mazauna wannan gunduma ta tsaunukan Qinling, wurin da ke matsayin wata iyaka tsakanin arewaci da kudancin kasar Sin. Shanyang ya samu kubuta daga kangin talauci a shekarar 2020.
Bayan kakkabe kangin talauci baki daya, yanzu haka gundumar ta samu karin damar mayar da hankali ga samar da kayayyakin motsa jiki, a wani mataki na kara inganta rayuwar al’ummar ta.
Da misalin karfe 8:30 na safe, masu hawa tsaunuka suka gangaro daga sabuwar hanyar hawa tsauni da aka gina a gandun Cuiping. Baya ga hanyoyi biyu na hawa tsaunukan Cuiping da Canglong, da kuma hanyar kafa ta gefen kogi da aka gina mai tsawon kilomita 8.5, akwai kuma wata mai nisan kilomita 2 da ake ginawa yanzu, a cewar Wang Linpei, jami’i a cibiyar wasanni ta gundumar.
Wang ya kara da cewa "Akwai wurin motsa jiki 1, kusa da duk nisan tafiyar mintuna 10 a wannan yanki" kuma "gudu da hawa tsaunuka, sun zama wasanni da mutane masu yawa ke yi a wannan yanki."
Bayan gama wasan kwallon tebur, Peng na halartar wata kwaleji ta dattawa, wadda aka tanada domin horas da dattijai dake yin kwasa-kwasai da ba na digiri ba. Yanzu haka yana karantar wasan erhu, da wasan violin na Sin, da wasan opera, yayin da kuma matarsa ke koyon darussan rawa. Ma’auratan ba sa komawa gida sai bayan karfe 11:00 na rana.
Da karfe 2:30 na rana kuma, ana fara buga wasan kwallon kwando a dakin motsa jiki na makarantar Middle dake Shanyang. Dalibai da dama na shiga a fafata da su a wannan filin, wanda kuma ake bude shi ga kowa da kowa kyauta.
Yayin da mafi yawan al’ummun yankin ke tashi daga aiki da karfe 5:00 na yamma, wasu daga mazauna yankunan birni da kauyukan dake kusa, suna isa cibiyar wasanni dake yammacin gundumar. A bara ne aka bude wannan cibiya, an kuma samar da kayan motsa jiki a cikin ta, ciki har da na wasan takalmin taya, da kwallon kwando da kwallon tebur.
Duk da yamma ta yi, masu wasan kwallon tebur a wannan gunduma ba su hakura ba. A wannan lokaci, rukunin yara ne ke buga kwallon. Ana bude ba da horo a kullum, ga rukunin wadannan kananan yara na kungiyar Zhengyang tun daga karfe 7 na dare.
Kocin kungiyar Chen Zhengzong, ya ce "Mai yiwuwa nan gaba su ne wadanda za su zamo zakaru a wasan ping pong, duba da cewa a bara ma, daya daga ‘yan wasan wannan kungiya ya samu shiga kulaf din lardin mu."
Zhang Wenqi, mai shekaru 10 da haihuwa, yana wasan kwallon tebur na sa’oi 2 a duk rana. Ya ce yana fatan zama zakaran duniya a wasan, kamar dan wasan kasar Sin Xu Xin.
Bayan yaran sun kammala na su horo da misalin karfe 9 na dare, Li Anmin, wanda shi ne shugaban kungiyar ‘yan wasan Badminton na gundumar, tare da abokan wasan sa, na fara buga wasa a dakin wasa dake kusa da wannan.
Li Anmin ya ce "Mu kan yi wasa tsakanin karfe 9:00 zuwa 11:00 na dare,". Li na cike da farin cikin ganin ‘yan wasan Bidminton sun karu daga mutum kusan 30 a shekarar 2009 zuwa mutum 139 a yanzu.
A wajen filin wasan, farfajiyarsa ta dau haske, inda mutane da dama ke koyon wasan fada na Sin, akwai kuma wasu yara dake koyon wasan taekwondo.
Li Anmin ya ce, ana sa ran fara amfani da wurin ninkaya dake cikin cibiyar a watan Afirilu dake tafe, yayin da kuma nau’oin wasanni da jama’ar yankin ke gudanarwa za su kai 11.
A cewar mataimakin daraktan hukumar wasanni ta wannan gunduma Xiao Xucheng, a ko wane mataki na shekaru, ko kwarewa mutumin Shanyang ke kai, ko da yaushe akwai nau’in wasa da zai dace da shi".