logo

HAUSA

Kakakin CMG:Ba wanda zai ji tsoron kalaman rashin hankali da Jam’iyyar DPP ta yankin Taiwan ta yi

2021-03-26 19:30:29 CRI

Kwanan baya, kakakin kwamitin Taiwan dake kula da harkokin babban yankin kasar Sin ya tsorata wasu mawaka da masu wasan kwaikwayo na yankin Taiwan cewar, “za a yanke hukunci kan wadanda suka keta dokoki”, kan wani bidiyo da suka dauka na rediyo da kafa mai alaka da shafin Intanet na musamman don watsa labarai ga yankin Taiwan na kasar Sin.

Dangane da wannan batu, kakakin cibiyar tsara shirye-shiryen da ake watsa wa yankunan Hong Kong, da Macao, da kuma Taiwan ta babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) ya bayyana cewa, yin mu’amala a tsakanin yankin Taiwan da babban yankin kasar Sin ya dace da bukatun al’umma da halin da ake ciki, kuma ba wanda zai iya hana wannan aiki.

Kalaman da Jam’iyyar DPP mai mulkin yankin Taiwan ta yi ta bata ran al’ummomin yankin Taiwan na kasar Sin da ma al’ummomin babban yankin kasar Sin, a don haka, dole ne, jam’iyyar ta daina tsorata mutane, ta kuma ba da gudummawa yadda ya kamata a fannin karfafa hadin gwiwar dake tsakanin al’ummomin yankin Taiwan na kasar Sin da na babban yankin kasar Sin, domin neman ci gaba tare. (Maryam)