logo

HAUSA

Wani rahoto da ya kunshi karairayi da yawa

2021-03-26 20:47:58 CRI

Wani rahoto da ya kunshi karairayi da yawa_fororder_0326-sharhi-Bello(1)

Tun daga farkon watan Maris da muke ciki har zuwa yanzu, kamfanin gidan telabijin na kasar Amurka CNN, da jaridar Guardian ta kasar Birtaniya, da wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya, suna ta kokarin yada labarai game da yadda aka gabatar da wani rahoto, wai ya kasance “rahoto mai zaman kansa na farko da ya shafi jihar Xinjiang ta kasar Sin”. Kana bisa wannan rahoto ne, wadannan kafofin watsa labarai suna zargin gwamnatin kasar Sin da neman “kawar da wata kabila daga doron kasa” a jihar Xinjiang.

A cewar wadannan kafofin watsa labaru, rahoton da aka gabatar da shi a ranar 8 ga watan Maris, ya kunshi sakamakon nazari masu zaman kansu da wasu masana na kasashe daban daban fiye da 10 suka yi. Kana marubutan rahoton su ma sun bayyana kansu da “nuna gaskiya da adalci”, kuma “ba tare da karkata ga wani bangare ba”. Sai dai, idan mun dan yin bincike kan matsayin marubutan rahoton, za mu iya ganin cewa, yadda suka bayyana kansu a matsayin “masu gaskiya da adalci”, karya ce.

Babban marubucin wannan rahoto game da jihar Xinjiang shi ne wani mutum mai suna Yonah Diamond. Idan mun yi bincike kan tarihin mutum, za mu san yana dauke da ra’ayin na matukar kin jinin kasar Sin. A kwanakin baya ya taba yin kira ga gwamnatin Joe Biden don ta dauki wasu matakai na kashin kai wajen tankiya da kasar Sin, da kara kakabawa kasar Sin takunkumi. Kana sauran “kwararru” na cibiyar nazari ta “Newlines” da suka taimakawa rubuta wannan rahoto sun hada da mambobin hukumar neman yin fito-na-fito da kasar Sin ta “Inter-Parliamentary Alliance on China” ta kasar Amurka, da tsoffin jami’an majalisar gudanarwar kasar Amurka, da mutane masu neman ganin kasar Amurka ta yi shishigi cikin harkokin sauran kasashe ta matakan soja. Ban da wannan kuma, an rubuta wannan rahoto ne bisa tushen “sakamakon nazari” na Adryan Zenz, wani mutum dake kaifin kishin addinin Kirista mai ra’ayin rikau. Duk wani sakamako na “nazari ” da mutum ya yi kan kasar Sin, ya kan kunshi dimbin karairayi, da bayanan jabu da ya gabatar ta hanyar sarrafa wasu alkaluma.

Yadda aka tsara rahoton bisa tushen maganganun Adryan Zenz ba wani abu ban mamaki ba ne, idan an lura da yanayin bangaren da ya ba da kudi don tallafawa aikin rubuta rahoton, wato jami’ar Fairfax ta kasar Amurka, wadda ke mallakar cibiyar nazari ta “Newlines”. Wannan jami’a sam ba ta da inganci, inda hukumar sa ido ta kasar Amurka ta taba rufe ta a shekarar 2019, bisa dalilin “malaman jami’ar ba su da izinin koyar da darassi”, kana “jami’a ta kasa tabbatar da ingancin nazarin da ake yi”. Ban da wanna kuma, jami’ar ta ba dalibanta damar yin magudin jarrabawa. Hakika, wasu kwanaki kafin cibiyar nazari ta Newlines dake karkashin jami’ar ta gabatar da wannan rahoto, wani kwamiti mai ba da shawara ga ma’aikatar ilimi ta kasar Amurka ta bukaci a dakatar da ayyukan jami’ar Fairfax, lamarin da ya sanya jami’ar sake fuskantar yiwuwar rufewa. Ga wannan jami’a maras inganci, da wata cibiyar nazari mai kunshe da “kwararru” masu nuna kiyaya ga kasar Sin, masu kallo, ko kuna tsammanin za su iya gudanar da bincike cikin adalci, ba tare da dora laifi ga wani da gangan ba?

Abin ban mamaki shi ne, kafofin yada labarai na kasashen yammacin duniya sun ki tantance maganganun da aka fada, kafin a fara watsa wannan rahoto zuwa kasashe daban daban. Kawai suna tsayawa kan ra’ayinsu na nuna bambanci kan kasar Sin, musamman ma a fannin tunanin siyasa. Don kare tunani na kansu, kofofin yada labarai na kasashen yamma sun yi kokarin yada jita-jita, da karairayi, tare da nuna goyon baya ga matakan takunkumi da wasu kasashen yamma suka sanya wa kasar ta Sin. A ganinku, shin ana iya amincewa da wadannan kafofin watsa labaru?

Saboda haka, idan kun samu ganin wasu labarai masu alaka da jihar Xinjiang ta kasar Sin, bari ku tantance daga ina aka fara samun wannan rahoton. Kar a bar wasu kafofin watsa labarai na kasashen yamma suka yaudare ku. (Bello Wang)

Bello