logo

HAUSA

Bai Kamata Yarjejeniyar BIT Ta Zama Wani Makami Na Wasu ’Yan Siyasan Yammacin Duniya Wajen Matsawa Sin Lamba Ba

2021-03-25 21:05:14 CRI

Bai Kamata Yarjejeniyar BIT Ta Zama Wani Makami Na Wasu ’Yan Siyasan Yammacin Duniya Wajen Matsawa Sin Lamba Ba_fororder_微信图片_20210325210441

Kwanan baya, kasar Sin ta mayar da martani ga kungiyar tarayyar Turai dangane da takunkumin da ta kakabawa wasu kamfanoni da daidaikun mutanen kasar Sin, sa’an nan, majalisar dokokin Turai ta sanar da soke taron bitar yarjejeniyar zuba jari tsakanin Sin da Turai wato BIT, domin matsa wa kasar Sin lamba.

Dangane da wannan batu, kasar Sin tana fatan kasashen Turai za su yi tunani kan abubuwa guda biyu.

Da farko, yarjejeniyar zuba jari tsakanin Sin da Turai yarjejeniyar ce da za ta amfanawa bangarorin biyu, wadda ta dace da bukatun Sin da Turai wajen habaka kasuwanci da samun karin jari, a maimakon tallafi da Turai ta baiwa kasar Sin. Dakatar da tattaunawa kan yarjejeniyar ba zai taimakawa kasashen Turai ko kadan ba.

Na biyu shi ne, abin da ya hana kulla yarjejeniyar zuba jari tsakanin Sin da Turai shi ne masu neman bata hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen Turai domin lalata alakar bangarorin biyu.

Yarjejeniyar zuba jari tsakanin Sin da Turai tana da burin samar da daidaito da bunkasuwa mai inganci, domin cimma moriyar juna. Bangarorin biyu sun yi alkawarin habaka hadin gwiwa mai inganci da kuma tallafawa juna, kuma dukkanin ka’idojin da aka tsara ya dace da bukatun bangarorin biyu. Yarjejeniyar za ta samar da adalci ga kamfanonin Sin da Turai, wadda za ta samar da tallafi ga kamfanoninsu, har ma ga kamfanonin kasa da kasa.

Yanzu, wasu ’yan siyasan yankin Turai suna neman siyasantar da wannan batu na tattalin arziki da ciniki, da kuma hana kulla yarjejeniyar zuba jari, bisa mugun burinsu na nuna kiyayya ga kasar Sin, tabbas, matakin zai haddasa asara ga kamfanonin kasashen Turai da ma al’ummominsu. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)