logo

HAUSA

Samar da karin ababen more rayuwa a Jihar Xinjiang alama ce ta muhimmanci da gwamnatin Sin ke dorawa ga ci gaban jihar

2021-03-25 18:49:40 CRI

Samar da karin ababen more rayuwa a Jihar Xinjiang alama ce ta muhimmanci da gwamnatin Sin ke dorawa ga ci gaban jihar_fororder_sharhi 25 03 21

Wasu rahotannin baya bayan nan na cewa, Jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta dake arewa maso yammacin kasar Sin, a bana za ta zuba jarin sama da kudin Sin har RMB yuan biliyan 240, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 36.8, a fannin samar da karin manyan ababen more rayuwar jama’a, da yawansu zai kai kimanin 350.

Bisa tsarin ayyukan da za a aiwatar a shekarar ta bana a wannan fanni, akwai kudaden da za a yi amfani da su wajen gudanar da ayyukan gona, da yawon bude ido, yayin da jihar ke burin jan hankalin sama da masu yawon bude ido miliyan 200 a bana, ya zuwa mutum miliyan 400 a shekarar 2025.

Ko shakka babu, wadannan ayyuka muhimmai, za su taka rawar gani wajen ingiza bullar sabbin guraben ayyukan yi, da fadadar manyan ayyuka a bangarori masu tasowa ko sabbin sana’o’i.

Kaza lika a wannan gaba da kasar Sin ke kara kyautata raya fannin noma, wannan tsari na zuba jari wajen samar da karin manyan ababen more rayuwa, ciki har da bangaren noma, zai bunkasa nasarar babban burin mahukuntan kasar, na daga matsayin samar da isasshen hatsi, baya ga karin kudaden shiga da kasar za ta samu ta hanyar fitar da albarkatun noma zuwa ketare.

Wani fanni muhimmi da wannan manufa ta shafa shi ne yawon bude ido. Ko shakka babu, bayan shawo kan annobar COVID-19 a sassan duniya daban daban, al’ummun kasashen duniya za su dora muhimmanci wajen yawon bude ido. Don haka inganta wannan tsari na samar da jari a fannin, musamman a wannan jiha ta Xinjiang, zai baiwa jihar damar cin gajiya daga babbar kasuwa ta cikin kasar, da ma kasuwar kasa da kasa.

Dukkanin wadannan alamu ne dake kara tabbatarwa duniya irin ci gaba da Jihar Xinjiang ke samu a shekarun nan, yana kuma kara haskaka muhimmancin da gwamnatin Sin ke dorawa ga ci gaban wannan jiha mai tarin kabilu, wadanda ke rayuwa cikin zaman lafiya da lumana. (Saminu Alhassan)

Bello