logo

HAUSA

CMG ya bude kafofin musamman na watsa labaru ga yankin Taiwan na kasar Sin

2021-03-24 21:36:45 CRI

A yau Laraba, babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG ya kaddamar da rediyo da kafa mai alaka da shafin Intanet na musamman don watsa labarai ga yankin Taiwan na kasar Sin. Inda shugaban hukumar kula da ayyukan rediyo da telabijin ta kasar Sin Mista Nie Chenxi, da shugaban CMG Mista Shen Haixiong da sauran manyan kusoshi suka halarci bikin kaddamarwar.

A jawabin da ya gabatar, shugaban CMG Shen Haixiong ya ce, kamfaninsa zai yi kokarin taimakawa tabbatar da hadin gwiwar al’ummun kasar Sin, da dikuwar kasar waje guda. (Bello Wang)

Bello