logo

HAUSA

Mutanen jihar Xijiang ta kasar Sin suna da damammaki na zabin ayyukan da suke so

2021-03-24 20:18:43 CRI

Mutanen jihar Xijiang ta kasar Sin suna da damammaki na zabin ayyukan da suke so_fororder_0324-sharhi-Bello

“Na zo nan aiki tare da mai gidana a shekarar 2018. A lokacin na ji an ce ana bukatar ma’aikata don gudanar da wasu ayyuka a wasu sassan kasarmu. Ina sha’awar wannan dama, don haka ni da mijina mun samu wani gurbin aikin yi.” Wata mace ’yar kabilar Uygur ce ta fadi haka, a cikin wani rahoton da jami’ar Ji Nan ta kasar Sin ta fitar a jiya Talata, kan yadda al’ummar jihar Xinjiang ke samun guraban ayyukan yi a wurare daban daban na kasar Sin.

Ba kamar yadda wasu mutane masu kin jinin kasar Sin na kasashe yammacin duniya, wadanda suka wallafa rahotanni bisa wasu karairayi ba, jami’ar Ji Nan ta kasar Sin ta gabatar da rahoton ne, bisa gudanar da cikakken bincike a wasu kamfanoni, ta kuma yi hira da wasu ma’aikata ’yan kabilar Xinjiang 70.

Daga wannan rahoton da aka gabatar, za mu fahimci cewa, mutanen jihar Xinjiang sun zabi gurbin aikin yi a wasu wurare ne bisa radin kansu, inda suke kokarin neman kyautata rayuwarsu, kana ba wanda ya tilasta musu yin aiki. Saboda haka, yadda wasu kasashen yammacin duniya suka kakaba takunkumi kan wasu kamfanonin kasar Sin, tamkar keta ’yancin yin aiki ne na mutanen jihar Xinjiang ta kasar Sin kawai.

Da ma hakki na rayuwa da neman raya kai, hakkin tushe ne na dan Adam. A baya jihar Xinjiang ta yi fama da matsalar hare-haren ta’addanci, lamarin da ya haddasa koma bayan tattalin arziki da zamantakewa a jihar. Ganin haka ya sa gwamnatin kasar Sin ta dauki jerin manufofin yakar ta’addanci a jihar, don tabbatar da kwanciyar hankali, da ci gaban tattalin arziki, gami da inganta zaman rayuwar jama’a.

Walwala da ci gaban da aka samu a jihar Xinjiang, ya nuna rashin dacewar matakin kakabawa jihar takunkumi, da wasu kasashen yammacin duniya suka dauka. Niyyarsu ita ce kawai neman hana kasar Sin samun ci gaba. Kuma tuni gamayyar kasa da kasa sun fahimci hakikanin nufinsu. (Bello Wang)

Bello