logo

HAUSA

Amurka ce babbar mai keta hakkin dan-Adam

2021-03-24 21:39:17 CRI

Amurka ce babbar mai keta hakkin dan-Adam_fororder_0324-Sharhi-Amurka-Ibrahim-hoto

A yau ne kasar Sin ta fitar da wani rahoto, game da yadda aka keta hakkin dan-Adam a kasar Amurka a shekarar 2020, inda a cikin rahoton aka gabatar da bayanai da shaidu wadanda ke bayyana yadda yanayin hakkin bil-Adam ya tabarbare a kasar ta Amurka.

Wannan zai baiwa duniya damar fahimtar cewa, yadda kasar dake daukar kanta a matsayin babbar kasa, take nunawa wasu kasashe yatsa da kakaba musu takunkumi babu gaira babu dalili, abin da ya sa ta zama wadda ta fi kowace kasa a duniya keta hakkin dan-Adam, kuma hakan babban barazana ne ga tsaro da kwanciyar hankali a duniya.

A shekarar da ta gabata, kowa ya ga rashin tabuka abin a zo a gani a fannin kare hakkin dan-Adam a bangaren Amurka. Yawan mutanen da annobar COVID-19 ta halaka a kasar, ya zarce 540,000, kana ana kara samun tashin hankali mai nasaba da kananan kabilu. Wadannan matsaloli, sun fito da manufurcin kasar kan batutuwan kare hakkin bil-Adama.

Abu mai muni, yayin da annobar COVID-19 ke ci gaba da addabar sassa daban-daban na duniya, har yanzu kasar Amurka na tsoma baki a harkokin cikin gidan wasu kasashe tare da sanya musu takunkumi babu gaira babu dalili, wai da sunan kare hakkin bil-Adama.

Bugu da kari, gwamnatin Amurka da ta gabata, ta yi watsi da matakai na kimiya, inda ta karkata ga manufar moriyar Amurka da farko, ta kuma mayar da kanta saniyar ware da ra’ayi na kashin kai, matakin da ya kasance babbar matsala da dunkulewar duniya wajen yaki da wannan annoba, da yadda take neman dora laifi kan wasu kasashe da ma WHO. Sai dai wannan dabi’a na Amurka ya gamu da Allah wadai daga kasashe da dama. (Ibrahim)