logo

HAUSA

Gyara dokar zaben yankin Hong Kong, harkar cikin gidan kasar Sin, bai kamata kasashen yamma su tsoma baki ba

2021-03-24 17:07:04 CRI

A shekarun baya, wasu bata-gari sun yi yunkurin balle yankin musamman na Hong Kong daga kasar Sin, da cin zarafi gami da lalata tambari har ma da tutar kasa, da zuga al'umma don su mamaye ofishin gwamnatin tsakiya dake Hong Kong, da kai harin kan mai uwa da wabi, da cin zarafin 'yan sanda wadanda a kullum suke sadaukar da rayukansu don tabbatar da tsaron al’umma, al'amuran da suka kasance ayyukan ta'addanci, da haifar da babbar barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a Hong Kong gami da cikakken iko na kasa.

Gyara dokar zaben yankin Hong Kong, harkar cikin gidan kasar Sin, bai kamata kasashen yamma su tsoma baki ba_fororder_20210324世界21010-hoto1

Amma duk wata kasa da ta san abin da take yi, ba za ta amince da irin wannan danyen aiki ba. Wai duk da sunan ‘yanci na demokiradiya. Kamar kowa ce kasa mai cikakken ‘yanci, ita ma kasar Sin tana da ‘yancin kafa dokokin da za su dace da yanayi da ma tsarin tafiyar da cikakkun yankunanta.

Wannan ya sa a shekarar da ta gabata, kasar Sin ta kafa, da fara aiwatar da dokar tsaron kasa mai nasaba da yankin Hong Kong. A wannan karon kuma, majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, ta amince da inganta tsarin dokar zaben yankin na Hong Kong, inda daga yanzu, masu kishin kasa ne kadai za su gudanar da harkokin zaben yankin.

Gyara dokar zaben yankin Hong Kong, harkar cikin gidan kasar Sin, bai kamata kasashen yamma su tsoma baki ba_fororder_20210324世界21010-hoto3

Yankin Hong Kong dai wani bangane na kasar Sin da ba za a iya raba shi ba. Harkokin Hong Kong, harkokin ne da suka shafi cikin gidan kasar Sin. Babu wata kasa da take da ikon tsoma baki a cikinsa, domin yin haka, ya saba ka’idoji da ma alakar kasa da kasa.

Masu fashin baki a ganin cewa, aiwatar da wannan doka, za ta kara tabbatar da manufar nan ta kasa daya, amma tsarin mulki iri biyu a yankin, baya da maido da cikakken zaman lafiya da wadata daga dukkan fannoni. Kuma duk wanda ya karya doka, tilas ne doka za ta yi aiki a kansa. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)