logo

HAUSA

Kalubalen Dake Gaban Shirin COVAX

2021-03-24 15:48:01 CRI

Kalubalen Dake Gaban Shirin COVAX_fororder_1

A yayin da kasashe masu tasowa ke ci gaba da karbar alluran riga kafin COVID-19 karkashin shirin nan na COVAX,shirin da aka bullo da shi domin ganin an samar da riga kafin dai-dai wa daida tsakanin kasashen duniya, da alamun yanzu ba a aiwatar da matakan raba rigakafin cutar COVID-19 daidai wa daida ba, wanda kuma masana ke cewa, hakan ko alama bai dace ba.

Daga cikin masu irin wannan ra’ayi har da babban darektan hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus, har ma ya yi kira da a hanzarta cike gibin adadin rigakafin da kasashe masu wadata ke yiwa al’ummunsu, da kuma wadanda ake samarwa kasashe marasa wadata karkashin shirin na COVAX. Idan ba haka ba, wankin hula zai kai duniya ga dare, a kokarin da ake yi na ganin bayan wannan annoba.

Babbar matsalar ita ce, yadda wasu manyan kasashe ke kokarin mallake rigakafi fiye da adadin da suke bukata don amfanin al’ummominsu, a don haka idan har duniya tana fatan yakar wannan annoba, to wajibi ne kasashe mawadata, su raba rigakafin da suke da shi da sauran sassan duniya karkashin shirin nan na COVAX, kana su ma kamfanonin dake sarrafa rigakafin su fadada samar da shi, ta yadda za a iya daidaita rabon sa tsakanin sassan duniya daban daban.

Haka kuma, ya kamata ragowar kasashe su yi koyi da kasar Sin, wadda tun farko ta yi alkawarin mayar da riga kafin zama hajar da al’ummar duniya za ta amfana da ita, baya ga yadda take tallafawa kasashe masu tasowa da riga kafin, ba tare da gindaya wani sharadi ba.

Shirin COVAX wanda ke gudana karkashin lemar WHO da abokan huldarta, an tsara shi ne da nufin tallafawa kasashe masu rangwamen karfi, ta yadda za su samu rigakafin cutar COVID-19 cikin sauki, kuma shirin na kara samun karin tagomashi a kullum.

Alkaluma na nuna cewa, ya zuwa yanzu shirin na COVAX ya raba sama da alluran rigakafin COVID-19 miliyan 30 ga kasashe fiye da hamsin. Sai dai duk da fa’idar wannan shiri, akwai sauran rina a kaba game da yadda kasashe marasa karfi za su kara cin gajiyarsa. (Ibrahim Yaya)