logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya mika sakon ta’aziyyar rasuwar tsohon shugaban kasar Tanzania

2021-03-23 19:32:26 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon ta’aziyya ga sabuwar shugabar kasar Tanzania, Madam Samia Sulhu Hassa, a yau Talata, don nuna alhinin rasuwar tsohon shugaban kasar John Pombe Magufuli.

Shugaba Xi na kasar Sin ya taya gwamnati da jama’ar kasar Tanzaniya, bakin ciki, tare da nuna juyayi ga iyalan marigayi John Magufuli, a madadin gwamnatin kasar Sin da jama’arta.

A cewar Xi, marigayi John Magufuli shugaba ne na kwarai, wanda ya ba da gagarumar gudunmawa ga kokarin karfafa hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da Tanzania. Rasuwarsa wata babbar asara ce ga daukacin al’ummun kasar Tanzania, kana Sinawa su ma sun rasa wani tsohon aboki. A cewarsa, kasar Sin na son ci gaba da zurfafa huldar hadin kai tsakanin kasashen 2, don amfanin jama’ar dukkan bangarorin 2. (Bello Wang)

Bello