logo

HAUSA

Ina dalilin karuwar hare haren garkuwa da mutane masu yawa a Najeriya?

2021-03-23 13:13:30 CRI

A cikin ‘yan shekarun da suka gabata, karuwar hare haren garkuwa da mutane sun karu a tarayyar Najeriya dake yammacin nahiyar Afirka, musamman ma harin masu yin awon gaba da jama’a da ‘yan bindiga sukan kaddamar a makarantun kasar, shin ina dalilin da ya sa haka?

A cikin watanni uku da suka gabata, dalibai da malamai na makarantun tarayyar Najeriya sama da 600 sun bace, sakamakon harin ‘yan bingida masu awon gaba da mutane, duk da cewa, laifuffukan sace sace sun dade suke faruwa a kasar, amma ana ganin cewa, matsalolin fama da talauci, da rasa aikin yi su ne suke haifar da laifuffukan awon gaba da mutane a kasar, kuma wadannan dalilai ne da suke janwo aukuwar hare-haren ta’addancin, da kungiyoyin masu tsattauren ra’ayi suka kan kaiwa wurare daban daban a fadin kasar.

Ina dalilin karuwar hare haren garkuwa da mutane masu yawa a Najeriya?_fororder_1

Tun daga watan Disambar bara, hare-haren sace daliban makaranta sun karu a bayyane a Najeriya, musamman ma a cikin watan Fabarairu da watan Maris da suka gabata. Alal misali, a ranar 15 ga watan Maris din bana, an yi awon gaba da malamai uku na makarantar firamare ta jihar Kaduna dake arewacin kasar, kuma a daren ranar 11 zuwa safiyar ranar 12 ga wata, wani gungun ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wasu daliban kwalejin nazarin gandun daji ta tarayya a garin Mando a jihar Kaduna dake arewa maso yammacin kasar, daga baya jami’an rundunar sojojin kasar sun ceto dalibai da malamai da yawansu ya kai 180, amma saura dalibai 39 sun bace. ‘Yan bindiga sun nemi a ba su kudin fansa da yawansa ya kai naira miliyan 500. An lura cewa, jihohin Kaduna, da Zamfara, da Naija da kuma Katsina, wadanda ke makwabtaka da juna sun fi shan wahalar harin ‘yan bindiga.

Rahotanni sun nuna cewa, Najeriya kasa ce mafi yawan al’ummu a nahiyar Afirka, kuma mutanen dake fama da talauci suna da yawan gaske a kasar, har gwamnatin kasar tama damuwa matuka kan matsalar. Wani rahoton da aka fitar a watan Oktoban shekarar 2020 ya nuna cewa, adadin mutanen dake fama da talauci mai tsanani a Najeriya ya kai miliyan 102, wadanda suka kai rabin al’ummun kasar, kuma ko wace rana kudin da suke kashewa bai kai dala 1.9 ba, kana wasu hukumomin ba da agaji na kasa da kasa ma sun nuna cewa, matsalar fama da talauci mai tsanani, ita ke hana ci gaban tattalin arzikin kasar ta Najeriya matuka.

Ina dalilin karuwar hare haren garkuwa da mutane masu yawa a Najeriya?_fororder_2

A ranar 23 ga watan Fabrairun bana, shugaban bankin raya Afirka ‘dan asalin Najeriya Akinwunmi Adesina, ya taba gabatar da wani jawabi, inda ya bayyana cewa, matsalar fama da talauci tana yin babban tasiri ga yanayin zaman takewar al’umma, da siyasa a kasar, haka kuma tana samar da damammaki ga kungiyoyin ta’addanci yayin da suke neman ‘yan ta’adda.

Adesina ya kara da cewa, matasa kaso 55 cikin dari ba sa iya samun aikin yi, a sakamakon haka, suna fama da talauci, duk wadannan sun haifar da aukuwar laifuffuka masu tarin yawa a kasar.

Hari la yau, tun bayan shekarar 2020, wato bayan barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19 a fadin duniya, tattalin arzikin Najeriya ya gamu da babbar matsala, haka kuma matsalar rashin aikin yi, da matsalar raguwar darajar kudi suna kara tsanantawa. Alkaluman da hukumar kididdigar kasar ta fitar a ranar 15 ga wata, sun nuna cewa, kason rashin aikin yi a kasar ya karu daga kaso 27.1 cikin dari a rubu’in biyu na bara, zuwa kaso 33.3 cikin dari na rubu’i na hudu na bara, lamarin da ya nuna cewa, al’ummun Najeriya da yawansu ya kai kusan miliyan 23 da dubu 190 sun rasa aikin yi, adadin da ya kai matsayin koli a cikin ‘yan shekarun da suka gabata.

Ina dalilin karuwar hare haren garkuwa da mutane masu yawa a Najeriya?_fororder_3

Ban da haka, alkaluman da hukumar ta fitar a ranar 16 ga wata, su ma sun nuna cewa, farasbin abinci a kasar ya karu bisa babban mataki, inda kuma darajar kudin kasar ta yi kasa da kaso 17.33 cikin dari a watan Fabrairun bana, kason da ya kai matsayin koli a cikin shekaru hudu da suka gabata. Duk wadannan na nuni da cewa, ‘yan bindiga na yin awon gaba da mutane ne kawai domin neman kudin fansa.

Ina dalilin karuwar hare haren garkuwa da mutane masu yawa a Najeriya?_fororder_4

Hakika, matsalolin talauci da rasa aikin yi, da koma bayan tattalin arziki, suna haifar da kalubalen tsaro a kasar, kuma gwamnatin kasar ta riga ta fahimci cewa, akwai bukata a yi kokari domin yaki da talauci, da samar da guraben aikin yi, da kuma raya tattalin arziki. A don haka shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sake jaddadawa, a taron kwamitin masu ba da shawara kan harkokin kasa da aka kira a ranar 23 ga watan Fabrairun bana cewa, duk da cewa aiki ne mai wahala, amma gwamnatin Najeriya za ta yi namijin kokari, na kubutar da al’ummun kasar da yawansu ya kai miliyan 100 daga kangin talauci.(Jamila)