logo

HAUSA

Masanin ilmin kayayyakin tarihi ya yabawa Sin bisa amfani da ta yi da sabbin fasahohi wajen nazarin kayayyakin tarihi

2021-03-22 14:26:38 CRI

Masanin ilmin kayayyakin tarihi ya yabawa Sin bisa amfani da ta yi da sabbin fasahohi wajen nazarin kayayyakin tarihi_fororder_0322-1

Gano wasu sabbin abubuwa a yankin tsohon ginin Sanxingdui mai dogon tarihi, dake lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar Sin ya jawo hankalin kasa da kasa sosai. Memban kungiyar hadin gwiwar nazarin kayayyakin tarihi ta kasar Masar, kuma forfesa a jami’ar Minia Ahmed Ata Derbala ya bayyana cewa, tawagar nazarin kayayyakin tarihi ta kasar Sin, ta yi amfani da sabbin fasahohi da na’urorin zamani wajen nazarin kayayyakin tarihi, da samun nasarori da dama a shekarun baya baya nan. Don haka kasar Masar tana son kara yin hadin gwiwa tsakaninta da kasar Sin a fannonin nazarin kayayyakin tarihi da tabbatar da su.

Farfesa Ata ya bayyana cewa, koda yake shi da kansa bai ziyarci kasar Sin ba, amma ya lura da ci gaban nazarin kayayyakin tarihi na kasar Sin. Wuraren kayayyakin tarihi na kasar Sin kamar su mutum-mutumin soja da dawaki na daular Qin, da babbar ganuwa, da yankin Sanxingdui, dukkansu sun yi suna a fadin duniya, wadanda suka wakilci dogon tarihi da al’adu na kasar Sin. Farfesa Ata ya bayyana cewa,

“Sin tana da albarkatun kayayyakin tarihi, kuma masu yawon shakatawa daga kasashe daban daban suna mamaki mamaki game da su. Kana daga abubuwan al’adu na kayayyaki, zuwa wadanda ba na kayayyaki ba, hukumomin al’adu na kasar Sin sun kare albarkatun al’adu da aka gaje su, da kuma gyara su yadda ya kamata, wanda ta hakan za a iya ci gaba da gadar su a kasar Sin.”

Farfesa Ata ya yi nuni da cewa, kasar Masar da kasar Sin suna da fifiko da fasahohi da dama wajen nazarin kayayyakin tarihi, ya kuma yabawa kasar Sin bisa amfani da take yi da sabbin fasahohi, wajen gano sabbin abubuwa a yankin tsohon ginin Sanxingdui, hakan ya inganta aikin nazarin kayayyakin tarihi zuwa wani sabon matsayi. Ya ce,

“Kasar Masar tana da albarkatun kayayyakin tarihi, a cikin wasu shekarun da suka gabata, tawagar nazarin kayayyakin tarihi ta kasar Masar ta gano sabbin abubuwa sau da dama a wuraren Saqqara, da Luxor, da Minia da sauransu, wadanda suka shaida cewa, kasar Masar tana da fasahohin nazarin kayayyakin tarihi. Kana kasar Sin ita ma tana da tawagar masu nazarin kayayyakin tarihi mai kyau, kungiyar kasar Sin ta yi amfani da sabbin fasahohin nazarin kayayyakin tarihi, da na’urorin zamani, wajen gudanar da nazari a wurin tarihi, da tabbatar da tarihin kayayyakin tarihi, don haka Sin ta samu nasarori da dama a wannan fanni a shekarun baya baya nan. Idan kasar Masar da kasar Sin za su yi hadin gwiwa kan masana da fasahohi a fannin nazarin kayayyakin tarihi, hakan zai sa kasashen biyu su samu ci gaba a wannan aiki.”

Farfesa Ata ya bayyana cewa, cutar COVID-19 da ta auku a shekarar bara, ta kawo illa ga zaman rayuwar jama’ar duniya, amma kasashen Masar da Sin, ba su dakatar da aikin nazarin kayayyakin tarihi ba. A yayin da ake bin matakan kandagarki cutar, sun ci gaba da yin nazarinsu tare da samun wasu nasarori. A wasu watannin da suka gabata, kasashen biyu sun gabatar da sabbin nasarorin da suka samu wajen nazarin kayayyakin tarihi. A watan Nuwanba na shekarar bara, kasar Masar ta sanar da gano sabbin busassun gawawakin mutane fiye da 100, wadanda aka kiyaye su da kyau har na tsawon shekaru 2500, a wurin Saqqara dake dab da birnin Alkahira, wanda shi ne aikin gano kayan tarihi mafi girma a kasar Masar a shekarar 2020.

Farfesa Ata ya bayyana cewa, a matsayin su na kasashe mafi tsayin tarihi da al’adu a duniya, hadin gwiwar dake tsakanin kasar Masar da kasar Sin a fannin nazarin kayayyakin tarihi, ya zama muhimmin fanni yayin da kasashen biyu suke yin hadin gwiwa da mu’amala da juna, don haka yana fatan kasashen biyu za su kara yin hadin gwiwa a fannonin nazarin kayayyakin tarihi, da tabbatar da su a nan gaba. Ya ce,

“Ina fatan kasashen Masar da Sin za su kara yin shawarwari da hadin gwiwa a fannin kiyaye al’adunsu. Kasashen biyu dukkansu suna da abubuwan tarihi da al’adun gargajiya da dama da aka gaje su daga kaka da kakani, kuma hadin gwiwar su a aikin kiyaye al’adu, zai samar da gudummawa ga tabbatar da al’adun duniya, kana zai kara sada zumunta a tsakanin jama’ar kasashen biyu. Na yi imanin cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Masar da Sin a fannin nazarin kayayyakin tarihi zai zama misali, na hadin gwiwar al’adu bisa tsarin shawarar ‘ziri daya da hanya daya’.”(Zainab Zhang)