logo

HAUSA

Masanin Burtaniya: JKS ta cimma nasarar gina al’umma mai matsakaicin wadata a dukkan fannoni

2021-03-22 19:36:50 CRI

Masanin Burtaniya: JKS ta cimma nasarar gina al’umma mai matsakaicin wadata a dukkan fannoni_fororder_0322-CPC-Ibrahim-hoto

Fitaccen masanin halayyar dan-Adam din nan dan kasar Burtaniya Martin Albrow, ya bayyana cewa, JKS dake shugabancin kasar Sin, CPC tana daf da kammala gina al’umma mai matsakacin wadata daga dukkan fannoni a wannan shekara, abin da ke zama wata babbar nasara.

Albrow ya bayyana haka ne, cikin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin. Masanin dai ya sha ziyartar kasar Sin tun a shekarar 1987.

Ya kara da cewa, a zahiri yake cewa, nasarar da JKS ta cimma, ta ciyar da kasar gaba, tare da cimma mafarkin kasar. Haka kuma nasarar JKS, babban sauyi ne kan yanayin da kasar take ciki.

Masanain ya ce, idan aka kalli yanayin jam’iyyar a cikin shekaru 100 na baya. Akwai shekarun da za a iya bayyanawa a matsayin karni na rashin jin dadi. A don haka, yanayin kasar ya farfado. Jam’iyyar ta samar da tabbaci da hadin kai, kuma wadannan manyan nasarori ne kan yanayin da kasar take ciki. (Ibrahim)