logo

HAUSA

Bai kamata ba a yi amfani da maganar fatar baki wajen kare hakkin jama’a

2021-03-22 19:56:56 CRI

Bai kamata ba a yi amfani da maganar fatar baki wajen kare hakkin jama’a_fororder_0322-sharhi-Bello

A karshen makon da ya gabata, an samu barkewar zanga-zanga a wurare daban daban na kasar Amurka, inda jama’a suka yi ta ihu don ganin an daina nuna kiyaya ga al’ummar kasar ’yan asalin yankin Asiya.

Lisa Ling, ’yar asalin Asiya ce kana wakiliyar gidan telabijin na CNN na kasar Amurka, ta taba bayyana cewa, yanzu ’yan asalin Asiya sun yi kama da dabbobin da suke jira a yanka su a kasar Amurka. Wasu abubuwan da suka abku a kasar a kwanakin baya, suna da tsoro, da ban mamaki, kamar yadda aka rika harbin wasu mata ’yan asalin Asiya 6 har suka mutu, da yadda aka doke wani tsoho mai shekaru fiye da 70 a duniya a kan titi, da kade wasu mata ’yan asalin asiya biyu da mota, kana maimakon a tsayar da motar nan take, sai aka ci gaba da tuka motar, tare da jan matan 2 a kasa, har sai da dukkansu suka mutu. Wadannan abubuwa sun nuna yadda ake kara kin jinin ’yan asalin Asiya a kasar Amurka.

Alkaluman na nuna cewa, tun daga watan Maris na shekarar 2020 zuwa watan Fabrairun shekarar 2021, an aikata laifufukan nuna kyama da bambanci ga ’yan asalin Asiya har sau 3795 a kasar Amurka.

Wannan babban dalilin da ya haifar da wannan matsala, shi ne yadda gwamnatin Trump ta yi kokarin yada jita-jita game da kasar Sin, da ta da rikici da kiyaya tsakanin al’ummu daban daban na kasar Amurka, bisa yunkurinta na kare moriyarta ta siyasa.

Antonio Gutteres, babban sakataren MDD, shi ma ya bayyana cewa, yadda ake yawan samun aikace-aikacen cin zarafin ’yan asalin kasasahen Asiya, wani nau’in ne na ra’ayin nuna bambancin kabilu a kasar Amurka, wanda ya alakanta cutar COVID-19 da nahiyar Asiya.

Ganin yadda yanayi ya tabarbare a kasar Amurka, ya sa manyan kusoshin kasar, ciki har da shugaban kasar Joe Biden, sun yi Allah wadai da aikace-aikacen karya doka. Sai dai har yanzu ba a ga wani takamaiman matakin da suka dauka don tabbatar da kare hakkin dan Adam na al’ummun kananan kabilu ba. A don haka, za mu iya ganin cewa, daliln da ya sa kasar Amurka ke fama da matsalar ra’ayin nuna bambanci ga kabilu daban daban har zuwa yanzu, shi ne domin manyan jami’an kasar, ba su da cikakkiyar niyyar daidaita wannan matsala. (Bello Wang)

Bello