logo

HAUSA

Idan ka kamu da ciwo, kada ka umarci wani ya sha magani

2021-03-21 21:30:09 CRI

Idan ka kamu da ciwo, kada ka umarci wani ya sha magani_fororder_20210321-sharhi-Sanusi Chen-hoto3

A ranar 16 ga wannan wata, an samu matsalolin harbe-harbe sau 3 a yankin Atlanta dake jihar Georgia, inda aka hallaka mutane 8, ciki har da matan Asiya 6. Lamarin ya girgiza duk duniya baki daya. Ko da yake wadanda suka haifar da laifin sun musunta cewa laifinsu ba shi da alaka da “nuna kabilanci”, amma mata 6 su ’yan Asiya ne, wannan ya shaida cewa, ’yan Asiya dake zaune a kasar Amurka sun sake zama mutanen da ake nunawa kiyayya sakamakon barkewar annobar Covid-19.

A waje daya kuma, a kasar Amurka, a kan keta ’yancin Amurkawa masu asalin Afirka da musulmai. A shekarar 1963, Martin Luther King Jr, ya bayar da wani jawabi mai taken “Ina da wani buri”, inda ya nuna fatansa na neman samun zaman daidai wa daida tsakanin bakaken fata da fararen fata. Ko da yake jawabinsa ya yi tasiri sosai ga daukacin al’ummar Amurka, amma ya zuwa yanzu, kusan shekaru 60 sun wuce, a kullum ana samun matsalolin nuna karfin tuwo da ’yan sandan fararen fatan Amruka su kan nuna wa bakaken fata. Alal misali, matsalar kisan George Floyd, wani dan Afirka dake zaune a Amurka da wani dan sandan farin fata ya yi masa.

Idan ka kamu da ciwo, kada ka umarci wani ya sha magani_fororder_20210321-sharhi-Sanusi Chen-hoto1

A kasar Amurka, fararen fata suna nuna kiyayya ga kananan kabilu, musamman mutanen da ba fararen fata ba, ya riga ya zama wata al’ada. Idan wani lamari, kamar yaki, ko matsalar rashin aikin yi, da barkewar wata annoba, ko ta’addanci ya faru, a kullum mutanen da ba fararen fata su ne kan zama masu rigar laifi.

Ko shakka babu, a kasar Amurka, Barak Obama, dan asalin Afirka ya taba zama shugaban kasar, Kolin Powell, da Condoleezza Rice da Lloyd Austin, ’yan asalin Afirka sun zama ministocin gwamnatin Amurka a lokuta daban daban, har ma madam Elaine Chao, da Mr. Jim Yong Kim wadanda suka fito daga yankin Asiya sun kuma hau kan mukaman ministoci a gwamnatin kasar Amurka, ko shugabancin Bankin Duniya, amma kamar yadda Mr. Thomas Sowell, farfesa mai nazarin ilmin tattalin arziki a kasar Amurka ya nuna a cikin littafinsa mai taken “Takaitaccen tarihi kan yadda ake nuna kabilanci a kasar Amurka”, cewar “a kasar Amurka, launin fata yana da muhimmanci sosai wajen kudurta makomar wani mutum.”

Ko da yake, matsalar nuna kabilanci ta tsananta sosai a kasar Amurka, amma har yanzu wasu ba su mai da hankali sosai kan batun kamar yadda ya kamata ba. A ranar 19 ga wannan watan na Maris, a lokacin da take muhawara da Mr. Dai Bing, mataimakin wakilin kasar Sin dake MDD, jakada Linda Thomas-Greenfield ta kasar Amurka dake MDD ta ce, nuna kabilanci a kasar Amurka ya kasance kamar “wani kalubale ne kawai da ake fuskanta a kullum”. Lalle a ganinta, wannan ba wata matsala mai tsanani ba ce. Sabo da haka, ba ta da kunya ko kadan, ta ce, “muna kokarin daidaita irin wanannan matsala, za mu ci gaba da yin haka.” Wallahi, ina son tambayar madam Linda Thomas-Greenfield, daruruwan shekaru sun wuce, me gwamnatocin kasarku suka daidaita kan batun? Ke ma ’yar asalin Afirka ne, ko maganarki za ta iya samun amincewa daga wajen ’yan uwanki na Afirka?

Idan ka kamu da ciwo, kada ka umarci wani ya sha magani_fororder_20210321-sharhi-Sanusi Chen-hoto2

Ya kamata ku tashi daga barci, ’yan siyasan Amurka da mutane wadanda aka cuce su. Kamar yadda jakada Dai Bing ya ce, “Idan kasar Amurka ta mai da hankalinta kan batun hakkin dan Adam cikin sahihanci, ya kamata ku daidaita matsalolin nuna kabilanci, da rashin adalci da muggun matsalolin da ’yan sanda suke aikatawa a yankin kasarku.” Bai kamata ku sa ido kan harkokin cikin gidan sauran kasashen duniya ba, har ma kun sanya laifiin “kisan gillar al’umma” ko “nuna kiyayyar dan Adam” ga kasashe wadanda suka samu nasara sosai wajen daidaita harkokin cikin gidansu. Wasu ’yan siyasan Amurka da masu tsattsurar ra’ayi na fararen fata, su ne ke da laifin “kisan gillar al’umma” da “laifin nuna kiyayyar dan Adam”. Idan kun kamu da ciwo, kada ku umarci wani ya sha magani. (Sanusi Chen)