logo

HAUSA

Hadin gwiwar cin moriyar juna ko gaba da juna?

2021-03-20 22:17:27 CRI

Hadin gwiwar cin moriyar juna ko gaba da juna?_fororder_微信图片_20210320205307

“Muna fatan shawarwarin da muke yi su kasance cikin sahihanci. Amurka ba ta cancanci ta nuna raini da fifiko ba a yayin da take shawarwari da kasar Sin, al’ummar Sinawa ba su amince da hakan ba.” A ranar 18 ga wata, agogon wurin, Mr.Yang Jiechi, mamban hukumar siyasa na kwamitin kolin JKS wanda kuma shi ne darektan ofishin kwamitin harkokin waje karkashin kwamitin kolin JKS, ya mai da martanin ne ga bangaren Amurka kan yadda ta kalubalanci kasar Sin tare da zarginta ba tare da wani tushe ba.

A daidai lokacin da huldar Sin da Amurka ke cikin mawuyacin hali, ana sa ran shawarwarin da aka gudanar a wannan karo a tsakanin manyan jami’an kasashen biyu za su samar da makoma mai kyau ga huldarsu. Duk da haka, kafin a fara shawarwarin, Amurka ta dauki jerin matakan da ba su dace ba a yunkurin matsa wa kasar Sin lamba, kuma har zuwa lokacin da aka fara shawarwarin, a jawabin da bangaren Amurka ya gabatar wanda ya wuce tsawon lokacin da aka kayyade, ya sha zargin kasar Sin kan harkokin cikin gidanta da suka hada da batun Hong Kong da na Xinjiang da sauransu, don neman nuna fifikonsa a wajen shawarwarin. A hakika, jami’an kasar Sin sun kai wannan ziyara ta musamman birnin Anchorage na jihar Alaska ta Amurka bisa gayyatar da bangaren Amurka ya yi musu, tare da niyyar daidaita huldar da ke tsakanin kasashen biyu, amma daidai kamar yadda kakakin ma’aikatar harkokin waje ta kasar Sin, Mr. Zhao Lijian ya bayyana, “Alaska jiha ce dake arewacin Amurka, inda ’yan tawagar kasar Sin suka ji sanyin jihar, baya ga kuma yadda Amurka ta karbi bakinta.” Tambayarmu ita ce, ko da gaske ne Amurka tana da niyyar daidaita huldarta da kasar Sin a wajen shawarwarin?

Hadin gwiwar cin moriyar juna ko gaba da juna?_fororder_微信图片_20210320205318

Yau da kimanin shekaru 120 da suka wuce, wasu kasashe 11 sun tilastawa kasar Sin da a wancan lokaci ke da rauni, ta sa hannu kan “Final Protocol for the Settlement of the Disturbances of 1900”, wata yarjejeniya maras adalci wadda ta lalata ikon kasar Sin. Ga shi yanzu, kasar Amurka wadda ta fi karfi a duniya tana neman nuna fin karfinta a yayin shawarwari da kasar Sin, amma ba ta gane ba, lalle zamani ya kare da za a tilasta wa kasar Sin ta yi kome. Amurka ba ta cancanci ta nuna raini da fifiko ga kasar Sin ba, ya zama dole su zauna daidai wa daida da kuma mutunta juna, don daidaita sabanin da ke tsakaninsu.

Ranar 15 ga wata rana ce ta cika shekaru 10 da aukuwar rikici a kasar Syria. Yau kimanin shekaru 10 da suka wuce, yadda Amurka da ma sauran wasu kasashe sun sa hannu cikin harkokin kasar ya sa zanga-zangar da aka yi a kasar ta zamanto rikici da ya barke ta dukkan fannoni, wanda daga bisani ya zama yaki da ke tsakanin sassa daban daban a kasar. Yaki na ci gaba a yau, wanda ya riga ya halaka dubban daruruwan al’umma tare da raba miliyoyin al’ummar kasar da muhallinsu. Da Iraki da Afghanistan da Libya da Syria, Amurka ta sha fakewa da sunan ’yanci da dimokuradiyya don sa hannun harkokin cikin gida na wasu, inda ya jefa kasashen cikin rikici da yaki, ga shi yanzu, tana neman ganin hakan ma ya faru a kasar Sin, sai dai ba za ta cimma burinta ba, sabo da al’ummar Sinawa ba mu yarda ba, kuma kamar yadda mamban majalisar gudanarwar wanda kuma shi ne ministan harkokin waje na kasar Sin, Mr.Wang Yi ya bayyana a yayin halartar shawarwarin, ya kamata Amurka ta “gyara halinta” na son sa hannu cikin harkokin cikin gidan kasar Sin.

Hadin gwiwar cin moriyar juna ko gaba da juna?_fororder_微信图片_20210320205255

Bayan da aka kammala shawarwarin, Mr. Yang Jiechi ya tattauna tare da manema labarai, inda ya ce, “shawarwarin na da amfani, wadanda za su taimaka ga inganta fahimtar juna. Sai dai har yanzu akwai sabanin ra’ayi a tsakanin kasashen biyu kan wasu batutuwa, kasar Sin za ta tsaya tsayin daka a kan matsayin kiyaye ikon kasar da tsaronta da kuma moriyarta ta samun ci gaba. Ba wanda zai iya hana ci gaban kasar Sin ba.”

Kasancewarsu kasashe biyu mafiya karfi a duniya, hadin kan Sin da Amurka zai amfana wa kasashen biyu, har ma duk duniya gaba daya. A yayin da kuma za su yi hasara in sun yi gaba da juna, kuma huldarsu ta haifar da babban tasiri ga duniya baki daya. Hadin kan juna zabi daya tilo ne ga kasashen biyu, kuma hakan zai iya tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a duniya. (Lubabatu)