logo

HAUSA

Sin ta nuna matsayarta a fannoni uku yayin tattaunawarta da Amurka

2021-03-20 20:41:30 CRI

Sin ta nuna matsayarta a fannoni uku yayin tattaunawarta da Amurka_fororder_1

An kammala tattaunawar yini biyu tsakanin manyan jami’an kasashen Sin da Amurka jiya a birnin Anchorage na jihar Alaskan kasar Amurka, wannan shi ne karo na farko da manyan jami’an kasashen biyu suka gudanar da tattaunawar fuska da fuska, tun bayan da sabon shugaban kasar Amurka Joe Biden ya kama aiki. Rahotanni sun nuna cewa, sassan biyu wato Sin da Amurka sun yi tattaunawa mai zurfi kan manufofin da kasashen biyu suke aiwatarwa a gida da waje, da huldar dake tsakaninsu, da kuma manyan batutuwan dake shafar shiyya shiyya da kuma kasa da kasa, duk da cewa, akwai sabani mai tsanani a tsakaninsu kan wasu bututuwa, amma sassan biyu suna ganin cewa, tattaunawar da suka yi tana da ma’ana, saboda ta kara zurfafa fahimtar juna a tsakaninsu.

A nata bangaren, kasar Sin ta nuna matsayarta a fannoni uku, na farko, ta je birnin Anchorage ne domin daidaita matsala, amma ba cacar baki ba. Yayin tattaunawar, kasar Sin ta mayar da martani da kakkausar murya domin bangaren Amurka ya zarge ta ba gaira ba dalili. Na biyu, duk da cewa, akwai sabani mai tsanani a tsakanin sassan biyu, kasar Sin tana kokarin gudanar da hadin gwiwa da Amurka. Na uku, kasar Sin ta bayyana matsayarta ta nacewa kan manufar gudanar da harkokin kasa da kasa tsakanin bangarori daban daban, inda ta yi nuni da cewa, ya dace a martaba ikon mulkin kasashe daban daban a duniya, da bambance-bambancen wayewar kai, ta yadda za a tafiyar da harkokin kasa da kasa bisa tsarin demokuradiyya.

Ana iya cewa, tsokacin da kasar Sin ta yi ya bayyana ra’ayoyin yawancin kasashen duniya, yanzu haka daukacin kasashen duniya suna fuskantar barazanar yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19, da sauran manyan sauye-sauye, ya zama wajibi kasashen duniya su yi kokari tare domin cimma burin samun bunkasuwa tare cikin lumana ta hanyar gudanar da hadin gwiwa, idan Amurka ba ta tafi da zamani ba, illar hakan za ta koma kanta.(Jamila)