logo

HAUSA

Yadda shugaban kasar Sin ya bayyana wa duniya mafarkin kasarsa

2021-03-19 14:29:34 CRI

“Mafarkin kasar Sin mafarki ne na dukkanin al’ummar kasar, haka kuma mafarki ne na kowane dan kasar.” A yayin bikin rufe taron shekara shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin da ya gudana a ranar 17 ga watan Maris na shekarar 2013, Mr. Xi Jinping wanda ya ci zaben shugabancin kasar ya gabatar da jawabi, inda ya sha ambaton “mafarkin kasar Sin” har sau tara a jawabinsa na tsawon minti 25, wanda ya samu tafi sosai daga mahalarta taron.

Mafarkin kasar Sin buri ne da al’ummar kasar ke neman cimmawa don inganta rayuwarsa, wanda kuma ke shafar burin da al’ummar duniya baki daya ke neman cimmawa. A cikin shekaru takwas da suka wuce, shugaba Xi Jinping ya sha bayyana wa duniya yadda mafarkin kasarsa ya kasance, tare kuma da bayyana matsayin da kasar ke dauka na kiyaye zaman lafiya da ci gaba, da kuma inganta hadin gwiwar cin moriyar juna. Ya ce,“Tabbatar da farfadowar al’ummar Sinawa, shi ne babban burin da al’ummar kasar suke fatan cimmawa a baya bayan nan, wanda muke kira “mafarkin kasar Sin, kuma ma’anarsa ita ce tabbatar da ci gaban kasa da farfadowar al’umma da inganta rayuwarsu.”

A watan Maris na shekarar 2013, a yayin da yake gabatar da jawabi a kwalejin nazarin huldar kasa da kasa ta birnin Moscow, shugaba Xi Jinping ya yi karin haske dangane da akidun mahukuntan kasarsa ta fannin gudanar da mulkin kasar. Kuma ita ce ziyara ta farko da Mr.Xi Jinping ya kai wata kasar ketare bayan da aka zabe shi a matsayin shugaban kasar Sin, inda kuma ya bayyana wa duniya cewa, mafarkin kasar Sin shi ne neman kiyaye zaman lafiya da ci gaba. Ya ce,“Bunkasuwar kasar Sin ta samar wa duniya karin damammaki a maimakon barazana. Mafarkin da muke fatan cimmawa ba kawai zai amfanawa al’ummar Sinawa ba, har ma da al’ummar kasashe daban daban.”

Haka kuma mafarkin kasar Sin mafarki ne da ke neman inganta hadin gwiwar cin moriyar juna. A watan Maris na shekarar 2014, a yayin taron cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da Faransa, shugaba Xi Jinping ya sake bayyana wa duniya yadda kasashen duniya za su amfana da mafarkin kasar Sin. Ya ce,“Mafarkin kasar Sin mafarki ne da ke samar da gudummawa ga duniya. Kamar yadda Sinawa kan ce, a yi kokarin gyara hali idan ana fama da talauci, kuma a yi kokarin ba da gudummawa ga sauran al’umma idan an samu nasara. Yadda kasar Sin ke dukufa a kan gudanar da harkokinta yadda ya kamata, taimakon kai ne baya ga gudummawa da ta samar ga kasashen duniya. A yayin da kasar Sin ke dada bunkasa, kasar za ta ci gaba da iyakacin kokarinta wajen ba da gudummawa ga kiyaye zaman lafiya da ci gaba a duniya.”

A watan Satumba na shekarar 2015, a yayin da yake gabatar da jawabi a gun taron hadin gwiwar kasashe masu tasowa karkashin MDD, ya bayyana yadda kasar Sin ke rungumar ‘yan Adam baki daya a mafarkinta, yana mai cewa,“Za mu ci gaba da hada bunkasuwarmu da bunkasuwar kasashe masu tasowa tare, sa’an nan, za mu hada mafarkin kasar Sin da mafarkin al’ummar kasashe masu tasowa na jin dadin zaman rayuwarsu, kuma har kullum za mu hada kai da kasashe masu tasowa, don samun ci gaba tare, ko kadan ba za mu sauya wannan matsayi ba, kuma har abada ba za mu sauya wannan manufa ba.”

A ranar 22 ga watan Oktoban shekarar 2015 kuma, shugaba Xi Jinping ya gabatar da jawabi a cibiyar hada-hadar kudi ta birnin London, inda ya yi nuni da cewa, kalubalen da duniyarmu ta fuskanta da ba ta taba garin irinta ba, ya zama dole kasashen duniya su hada kansu. Mafarkin kasar Sin mafarkin al’ummarta na jin dadin rayuwarsu ne, wanda kuma ke shafar kyawawan mafarki na al’ummar kasa da kasa. Ya ce,“Tabbas ci gaban kasar Sin wani bangare ne na ci gaban duniya, wanda kuma zai samar da karin kuzari ga ci gaban kasa da kasa da ma karin damammaki.”

Mafarkin kasar Sin mafarki ne na kasar, haka kuma na duniya baki daya. Kamar dai yadda shugaba Xi Jinping ya ce, yadda al’ummar kasar suka cimma mafarkinsu, tabbas zai samar da karin damammaki ga kasashe daban daban, tare kuma da inganta zaman lafiya da ci gaba a duniya.”(Lubabatu)