Malami mai aikin kiwon shanu
2021-03-19 11:59:09 CRI
Malam Yang Deqing dake kauyen Maha da ke gundumar Datong mai zaman kanta ta kabilar Hui da ta Tu na lardin Qinghai na kasar Sin. Kasancewar kauyensu yana cikin tsauni, karancin gonakin noma sun dade suna yi wa bunkasuwar kauyen tarnaki. Don haka, a cikin ‘yan shekarun baya, ya fara aikin kiwon shanu, aikin da ya samar masa tarin riba. Yanzu haka, yana kiwon shanu sama da 150, ya ce, “Aikin kiwon shanu ya kawo manyan sauye-sauye ga rayuwata, a wannan shekara, ina shirin gyara rumfunan shanu, har ma zan kara sayo wasu marakai.” (Lubabatu)