Shin Tattaunawa Tsakanin Manyan Jami’an Sin da Amurka Za Ta Kyautata Dangantakar Kasashen Biyu?
2021-03-19 19:43:51 CRI
Da karfe biyar na yammacin ranar 18 ga wata agogon Amurka, aka kammala taron na farko na tattaunawa tsakanin manyan jami’an Sin da Amurka, inda tawagar Sin wadda memban hukumar siyasa na kwamitin tsakiyar JKS, kuma shugaban ofishin kwamitin kula da harkokin waje na kwamitin tsakiyar jam’iyyar Yang Jiechi, da kuma memban majalisar gudanarwar kasar, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi suka jagoranci bangaren Sin, yayin da tawagar wakilan kasar Amurka ta kunshi sakataren harkokin wajen kasar Anthony Blinken, da mai bada shawara kan harkokin tsaron Amurka Jake Sullivan.
Bisa labarin da kafofin watsa labaru suka bayar, an ce, a yayin tattaunawar, bangaren Sin ya gabatar da matsayin kasar. Kuma Yang Jiechi ya yi fatan za a tattauna cikin sahihanci kuma a bayyane. Ya ce Sin da Amurka dukkansu manyan kasashen duniya ne, dukkansu suna daukar nauyin tabbatar da zaman lafiya da karko, da samun bunkasuwa a duniya.
Kafin tattaunawar, kasar Amurka ta sha yiwa kasar Sin matsin lamba kan batutuwa da dama, kamar game da yankin Hong Kong, da yankin Xinjiang, da kiyaye hakkin dan Adam, ta kuma sanya takunkumi ga wasu jami’an gwamnatin kasar Sin da sauransu, wanda hakan ya sa bangarori daban daban na kasa da kasa, suke nuna damuwa ga makomar tattanawar da aka yi a tsakanin Sin da Amurka.
A daya bangaren, yayin yake gabatar da jawabin farko na bude tattaunawar, bangaren Amurka ya zarce lokacin da aka kayyade masa, tare da gabatar da zarge-zarge marasa tushe, da sukar kasar Sin kan harkokinta na cikin gida dama na ketare. Sau da dama kasar Amurka ta tada zaune-tsaye kan kasar Sin, wanda hakan ya shaida cewa, Amurka ke jin tsoro da rashin tabbaci ga kasar Sin, kamar yadda Yang Jiechi ya fada, ba wanda ya baiwa Amurka izinin ba da umurni ga kasar Sin, kana jama’ar Sin ba su yarda da hakan ba. Kasar Sin tana mu’amala da sauran kasashe ne bisa ka’idar girmama juna.
Yayin da tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya kama mulkin kasarsa, an yi matukar lalata dangantakar dake tsakanin Amurka da Sin. Tun lokacin da Biden ya zama sabon shugaban kasar kuma, har yanzu ba a kyautata dangantakar sosai ba, domin sabuwar gwamnatin kasar ta ci gaba da aiwatar da manufofin da gwamnatin Trump ta tsara game da kasar Sin, wato dai manufofi iri daya amma hanyoyin aiwatar da su daban ne.
Amma a gaban kalubalen duniya kamar sauyin yanayi, da tinkarar cutar COVID-19, da farfado da tattalin arziki da sauransu, duniya ba za ta iya yin watsi da kasar Sin ba, don haka koda yake kasar Amurka ba ta son raya dangantakar dake tsakaninta da Sin, amma tilas ne Amurka na bukatar kasar Sin. A sakamakon la’akari da moriyar bangarori daban daban, Amurka ta bada shawarar yin tattaunawar manyan jami’an Sin da Amurka bisa manyan tsare-tsare ga kasar Sin, kana kuma Sin ta yarda da shiga tattaunawar bisa gayyatar da Amurka ta yi mata.
Gudanar da tattanawar ya shaida cewa, manyan kasashen biyu dake kan gaba a fannin tattalin arziki na duniya, suna kokarin daidaita matsalolinsu, da kyautata manufofin diplomasiyya, ana kuma iya cewa, wannan tattaunawa za ta zama sabon mafari na raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka.
Koda yake ba za a iya daidaita dukkan matsaloli ta tattaunawa sau daya ba, amma fara tattaunawa muhimmin mafari ne a wannan fanni. Mai yiwuwa ba za a cimma daidaito a dukkan fannoni a tattaunawa daya kawai ba, amma ana iya bullo da kyakkyawar alama ta daidaita matsalolinsu.
Ya kamata Sin da Amurka, su bayyana matsayinsu a fili, su yi musayar ra’ayoyi, da kara yin imani da juna, da yin bayani kan shakkun da suke nunawa juna, domin hakan zai taimaka musu, wajen warware matsalolinsu yadda ya kamata. (Zainab Zhang)