Yara suna jin dadin wasan tsallake igiya na nuna fasaha
2021-03-19 12:28:29 CRI
Yara dake makarantar firamare ta garin Huaining a lardin Jiangsu, suna jin dadin wasan tsallake igiya na nuna fasaha. An kafa kungiyoyin wasan 12, don dacewa da yanayin yara masu shekaru daban daban da haihuwa, ta yadda za su iya shiga wannan wasa cikin sauki.