logo

HAUSA

Masar ta kafa hukumar kula da wasan tseren kwale kwale tana kuma fatan karfafa alaka da Sin ta fuskar wasanni

2021-03-18 20:09:07 CRI

Masar ta kafa hukumar kula da wasan tseren kwale kwale tana kuma fatan karfafa alaka da Sin ta fuskar wasanni_fororder_0318-4

Mahukuntan kasar Masar, sun amince da kafa hukumar kula da wasan tseren kwale kwale, tare da fatan karfafa alakar kasar da Sin ta fuskar raya wasanni.

An kaddamar da hukumar ta EDBF ne, a gaban ginin wani otal dake birnin Alkahira, wanda ke kallon kogin Nilu, ana kuma fatan hakan zai kara dinke sassan kasashen biyu ta fannin raya wasanni.

Yayin kaddamarwar, an jera wasu kwale kwale masu siffar dabbar dragon, dauke da masu tuka su wadanda suka rika tsere, yayin da masu kallo ke Shewa da jinjina musu suna, ana kuma kada wasu ganguna.

A baya bayan nan ne dai ma’aikatar wasannin kasar Masar, ta amince da kafa hukumar ta EDBF, kana ita ma hukumar kasa da kasa mai kula da wasan wato “International Dragon Boat Federation ko IDBF, ta amince da kafuwar wannan hukuma ta Masar.

Da yake tsokaci game da kafuwar hukumar ta EDBF, shugaban ta Nader Roshdy, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, wasanni na da matukar tasiri na hade sassan kasashe waje guda, kuma a wannan gaba, tasirin sabuwar hukumar zai bunkasa karbuwar wasanni irin na Sin a Masar, tare da karfafa alakar al’ummun su.

A nasa bangaren, shugaban hukumar IDBF Mike Thomas, ya aike da sako ta bidiyo, na taya Masar murnar kafa wannan sabuwar hukuma. Yana mai fatan kasar wadda ke Arewacin Afirka, za ta ci gaba da ba da gudummawa wajen yayata wannan nau’in wasa a sassan kasashen Afirka, da kasashen larabawa, da duniya baki daya.

A nasa bangare, jakadan Sin a Masar Liao Liqiang, ya fitar da wata sanarwa, wadda aka karanta ga mahalarta bikin kafuwar sabuwar hukumar, inda a cikin ta ya bayyana matukar farin cikin sa da kafuwar hukumar ta EDBF, wadda ya ce za ta yayata wasanni da ke da tarihin shekaru 2,000 a duniya.

Jakada Liao ya kara da cewa, "Yayin da muke murnar shigar da wasan tseren kwale kwale, cikin jerin wasannin kasar Masar, mun kuma bude wani babi na kara fadada sadarwa, da curewar al’adun kasashen nan biyu wuri guda”. Liao ya kuma yi fatan ganin wannan mataki ya kara zurfafa alaka da kawancen dake tsakanin wadannan kasashe guda biyu.

Bisa tarihi, Ehab Gouda ne ya fara kai wasan tseren kwale kwale ko “Dragon boat” kasar Masar kusan shekaru 5 da suka gabata, kasancewar sa yana da matukar sha’awar wasan. Bayan fara gudanar da shi a Masar, sai Gouda tare da matarsa Mary Lai suka kafa kungiyar masu sha’awar wasan. Kafin hakan, Gouda ya samu horo game da wasan, ya kuma kware lokacin da yake shiga a dama da shi a Hong Kong, da kuma birnin Guangzhou. A yanzu haka kuma, Gouda wakili ne na hukumar IDBF, ya kuma shirya gasanni da dama a gida da kuma na kasa da kasa a Masar, tun daga shekarar 2016 zuwa yanzu.

Kafuwar EDBF wani mafarki ne da ya zama gaskiya, a cewar Mr. Gouda lokacin da yake zantawa da Xinhua, yana mai cewa wannan wasa ya zama wata gada tsakanin Masar da Sin, wanda zai kuma jawo karin masu yawon shakatawa Sinawa zuwa kasar Masar. Ya ce IDBF ta gayyaci Masar ta shiga gasar “dragon boat” ta kasa da kasa, wadda za ta gudana nan gaba a wannan shekara ta bana.

Iman Negm, sakatare ne a ma’aikatar raya al’adu ta Masar, ya kuma halarci bikin kaddamar da hukumar EDBF, inda ya bayyana alakar dake tsakanin Sin da Masar a matsayin ta musamman, yana mai jinjinawa bunkasar da ake kara samu a fannin musayar al’adu tsakanin kasashen biyu.

Baya ga jami’ai daga bangaren Masar, akwai kuma wasu baki Sinawa da suka halarci wannan biki.

Henrywoo Hon, dan kasuwa ne daga Hong Kong, wanda ya halarci wannan biki, ya kuma bayyana cewa, akwai hanyoyi da dama na bunkasa alakar kasashen biyu. A ganin sa, yayata wasa mai nishadantarwa kamar “dragon boat” daya ne daga hanyoyin sada al’ummun kasashen biyu da juna ta hanyar raya abota.

A daya bangaren kuma, ‘yan wasa masu yin wasan na tseren kwale kwale dake Masar, su ma sun jinjinawa kafuwar wannan hukuma ta EDBF, suna masu fatan nunawa duniya kwazon su, a fannin raya dukkanin gasannin “dragon boat” da za a gudanar a nan gaba.

Tarek Sami, matashi ne mai shekaru 26 a duniya, kuma wanda ke cikin daya daga kwale kwalen da aka yi amfani da su yayin kaddamar da sabuwar hukumar, ya kuma bayyana cewa, "Mun jima muna jiran kafuwar wannan hukuma a Masar, yanzu kuma muna farin ciki sosai da tabbatar wannan buri na mu.

Yayin wasan da aka gudanar lokacin kaddamar da sabuwar hukumar, dukkanin ‘yan wasa masu tuka kwale kwale daga bangarori 2 dake jere maza ne, in banda Marwa Mohamed, wadda ta jagoranci masu buga ganguna.

Matashiyar ta bayyana wannan wasa a matsayin mai kyawun gani da sa nishadi, wanda kuma ke koyarda hadin gwiwa da aiki tare, tana mai cewa, ta kwashe shekaru 3 tana samun horo a wasan. Marwa Mohamed ta kara da cewa wasan "Dragon boat” ba wasa ne kadai ba, domin kuwa ya kasance wata kafa ta musayar al’adu da sauran su.