logo

HAUSA

Dole a rarraba allurar rigakafin cutar COVID-19 bisa adalci

2021-03-18 19:17:07 CRI

Dole a rarraba allurar rigakafin cutar COVID-19 bisa adalci_fororder_1

A kwanakin baya shugaban kasar Mexico Andrés Manuel López Obrador, ya godewa kasar Sin, bayan da ya karbi tallafin allurar rigakafin cutar COVID-19, kuma a karo na farko, ya yi kirayi ga kasar Amurka, inda ya bayyana cewa, “Ina fatan zan samun damar nuna godiya ga gwamnatin Amurka, saboda na tabbatar da cewa, Amurka ita ma za ta samar mana taimako, duk da cewa, har yanzu ba ta yi hakan ba.”

Hakika kakakin fadar White House Jen Psaki, ta riga ta bayyana a fili cewa, kasashen duniya da dama sun bukaci Amurka da ta samar musu da tallafin allurar rigakafi, amma kawo yanzu gwamnatin Amurka ba ta fara samar da allurar ga sauran kasashe ba tukuna.

Matakin da Amurka ta dauka ya nuna cewa, tana aiwatar da manufar nuna fifiko kan al’ummun kasashe daban daban wajen rarraba allurar rigakafin, alkaluman da MDD ta fitar sun nuna cewa, allurar rigakafin cutar COVID-19 kaso 75 bisa dari, suna hannun kasashen duniya 10 ne kacal, kuma har yanzu kasashen duniya da yawansu ya kai 130 ba su samu allurar rigakafin ko daya ba.

Dole a rarraba allurar rigakafin cutar COVID-19 bisa adalci_fororder_2

Kana abun bakin ciki shi ne, wasu kasashe masu ci gaba, suna zargin allurar rigakafin da kasashen Sin da Rasha suka samar, sakamakon la’akari da moriyar tattalin arziki, haka kuma bayan da suka lura cewa, allurar rigakafin kasar Sin sun samu maraba matuka daga kasashen duniya da yawan gaske, sai suka fara baza jita-jitar wai kasar Sin tana son cimma yunkurin diplomasiyya ne, ta hanyar samar da allurar rigakafin, wato dai tana mayar da allurar matsayin wani makamin siyasa.

Amma abun farin ciki shi ne, har kullum kasar Sin tana yin kokarin rarraba allurar rigakafin bisa adalci, domin kandagarkin annobar a fadin duniya yadda ya kamata, kuma kasashen duniya da dama dake nahiyoyin Asiya, da Turai, da yankin Gabas ta Tsakiya, da Afirka, da Amurka, sun samu allurar rigakafin da kasar Sin ta samar. Kawo yanzu an yi wa shugabannin kasashe da dama allurar a fili, ana kuma iya cewa, suna goyon bayan kasar Sin ta hanyar yaba wa ingancin allurar rigakafin kasar.

Cikin kwanakin da suka gabata, kasar Sin ta samar da allurar rigakafin dubu 300 kyauta ga jami’an kiyaye zaman lafiya na MDD, kuma za a yi amfani da su ne a wuraren aikinsu dake Afirka. Duk wadannan sun nuna cewa, kasar Sin tana samar da allurar rigakafinta ga daukacin al’ummun kasa da kasa.

Kwayar cutar COVID-19 tana shafar daukacin kasashen duniya ne, don haka dole ne a yi kokarin kandagarkin annobar tare. (Jamila)