logo

HAUSA

An ba da iznin amfani da maganin cutar COIVD-19 na kasar Sin a kasashen Turai da Amurka

2021-03-17 11:35:34 CRI

An ba da iznin amfani da maganin cutar COIVD-19 na kasar Sin a kasashen Turai da Amurka_fororder_0317-1

A baya bayan nan ne kasashen Turai da Amurka suka ba da iznin amfani da wani sabon maganin cutar COVID-19 da kasar Sin ta samar. Bayan hakan ne kuma, wakilin CMG ya tattauna da wata shahararriyar masaniya mai nazarin kwayoyin halittu, mai suna Yan Jinghua, wadda ke cikin tawagar kwararrun da suka kirkiro sabon maganin.

A kwanakin nan, hukumar kula da magunguna ta nahiyar Turai ta ba da izni ga kasashen Turai su fara amfani da wata sabuwar fasahar tinkarar cutar COVID-19, inda za a yi amfani da magunguna LY-CoV555, da LY-CoV016 a lokaci guda. A cikinsu, LY-CoV016 wani magani ne da cibiyar nazarin kwayoyin halittu karkashin babbar cibiyar nazarin kimiyya da fasaha ta kasar Sin ta kikiro, bisa hadin gwiwa da kamfanin samar da magani na TopAlliance. Kafin haka kuma, a watan Fabrairun da ya gabata, hukumar sa ido kan abinci da magunguna ta kasar Amurka ta ba da iznin amfani da maganin LY-CoV016 a kasar.

An ba da iznin amfani da maganin cutar COIVD-19 na kasar Sin a kasashen Turai da Amurka_fororder_0317-2

Madam Yan Jinghua, daya ce daga cikin kwararrun masanan da suka kirkiro sabon maganin. A cewarta, sabon maganin zai yi amfani sosai a fannonin jinyar masu kamuwa da cutar COVID-19, da kare sauran mutane daga kamuwa da cutar. Ta ce,

“Kafin kwayoyin cutar COVID-19 su samu shiga cikin kwayoyin halittu, za su nemi wani sinadarin da zai taimaka wajen hada kwayoyin cuta da na halittu. Idan akwai wani magani da zai katse huldar kwayoyin cutar da kwayoyin halittun dan Adam, cutar ba za ta kama mutum ba. Hakan ya yi kama da yadda ake amfani da mabudi wajen bude makulli. Idan an toshe kofar makulli, to, mabudin ya zama mara amfani. Don haka, wannan magani zai iya kare dan Adam daga cutar COVID-19.”

Madam Yan ta kara da cewa, tun lokacin da aka fara samun barkewar annobar COVID-19, cibiyar nazarin kwayoyin halittu karkashin babbar cibiyar nazarin kimiyya da fasaha ta kasar Sin ta fara aikin kirkiro sabon maganin. Bisa fasahohin da cibiyar ta samu a fannin samar da maganin cututtuka masu yaduwa, da hadin gwiwa da wasu kamfanoni, an samu damar samar da maganin cikin sauri.

“Abun da ya fi wuya cikin ayyukan kirkiro maganin cuta mai yaduwa, shi ne gudanar da aikin cikin sauri. Sai dai tawagarmu ta dade tana kokarin kirkiro magungunan cutar Zika, da ta MERS, saboda haka mun kware a fannin tace kwayoyin halittun mutanen da suka warke daga cuta, don neman samun wasu sinadarai na maganin cututtuka. Sai dai ana bukatar gudanar da aikin cikin sauri. Yanzu mun kwashe kimanin shekara daya muna gudanar da bincike, daga baya an fara mika maganin ga kasuwannin kasa da kasa. Cimma wannan nasara ba wani abu mai sauki ba ne.”

A watan Maris na bara, cibiyar nazarin kwayoyin cuta karkashin babbar cibiyar nazarin kimiyya da fasaha ta kasar Sin ta ba kamfanin TopAlliance ikon samar da maganin LY-CoV016 ga kasuwa. Daga baya, kamfanin ya kulla yarjejeniya da kamfanin samar da magani na Eli Lilly na kasar Amurka, don gwajin maganin a aikin jinyar masu kamuwa da cutar COVID-19. Zuwa watan Yunin bara, hukumomi masu kula da magani na kasar Sin da na kasar Amurka dukkansu sun ba da iznin gwajin maganin. Abun da ya sanya maganin ya zama irinsa na farko, da aka fara gudanar da gwajinsa kan jikin dan Adam, bayan kammala gwaje-gwajensa kan dabbobi. A cewar Madam Yan, gwajin da aka yi ya samu wani sakamako mai yakini.

“Gwaje-gwajen da aka yi kan mutane masu kamuwa da cutar COVID-19 sun nuna cewa, ba wanda ya mutu, kana yawan mutanen da aka kwantar da su a asibiti, da na wadanda suka nuna wasu alamu masu tsanani sun ragu da kashi 70%. Wannan sakamakon da aka samu ya sa kungiyar tarayyar kasashen Turai da kasar Amurka ba da iznin amfani da maganin.”

Yan ta kara da cewa, matakan da aka dauka kan maganin na kasar Sin sun nuna cewa, kasashe daban daban sun yarda da ingancin maganin cutar COVID-19 kirar kasar Sin, da yadda yake da amfani wajen kare dan Adam daga wannan mummunar cuta. (Bello Wang)

Bello