logo

HAUSA

Matakin takunkumin dake shafar HK da Amurka ta dauka ba shi da wani tasiri ko kadan

2021-03-17 19:50:10 CRI

Matakin takunkumin dake shafar HK da Amurka ta dauka ba shi da wani tasiri ko kadan_fororder_1

A yau Laraba ne ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka, ta sanar da cewa, za ta sanya takunkumi ga wasu jami’an kasar Sin, saboda hannu da suke da shi wajen rage hakkin mazauna yankin Hong Kong na gudanar da harkokin yankin. Wannan mataki na nuna karfin tuwon da Amurka ta dauka, ya zamo tsoma baki ne a fili a cikin harkokin gida na kasar Sin, ya kuma sabawa babbar ka’idar dokokin kasa da kasa, da kuma huldar dake tsakanin kaashen duniya. Haka zalika, ya sabawa amanar al’ummun kasa da kasa, ko da yake matakin ba zai yi wani tasiri ba ko kadan ba.

Hakika Amurka, ta taba daukar irin wannan mataki kafin shekaru bakwai da suka gabata, inda ta sa hannu kan “dokar gudanar da harkokin yankin Hong Kong”, tare kuma da zargin dokar tsaron yankin Hong Kong, har ta yi kashedin cewa, za ta sanya takunkumi kan kasar Sin, daga baya ta dauki matakai a jere, amma dukkansu ba su yi amfani ba ko kadan.

Matakin takunkumin dake shafar HK da Amurka ta dauka ba shi da wani tasiri ko kadan_fororder_2

Yanzu haka Amurka ta sake daukar matakin sanya takunkumi maras tushe.

An lura cewa, tun bayan da aka dawo da yankin Hong Kong karkashin mullkin kasar Sin, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin tana aiwatar da manufar “kasa daya mai tsarin mulki biyu” a yankin, kuma tana yin amfani da manufar mazauna yankin su gudanar da harkokin yankin da kansu, kuma majaliar wakilan jama’ar kasar Sin ta kyautata tsarin yin zabuka a yankin, domin tabbatar da ikon mulkin gwamnatin tsakiya a yankin, tare kuma da martaba ikon tafiyar da harkokin yankin bisa doka.

Matakin takunkumin dake shafar HK da Amurka ta dauka ba shi da wani tasiri ko kadan_fororder_3

Abu mafi muhimmanci shi ne, ma’anar tsarin kasa daya mai tsarin mulki biyu, kasa daya ta fi muhimmanci, dole ne a gudanar da zabukan kananan gwamnatoci karkashin jagorancin gwamnatin tsakiya.

Yanzu haka, yawancin kasashen duniya suna goyon bayan kasar Sin, yayin da take aiwatar da manufofin dake shafar yankin Hong Kong, matakan da wasu ‘yan siyasar Amurka suka dauka wasan siyasa ne kawai, marasa amfani ko kadan.

Kasar Sin ba ta son ganin tsanantar huldar dake tsakaninta da Amurka, idan Amurka ba ta daina yin haka ba, kasar Sin za ta mayar da martani idan ta ga dama, domin kiyaye ikon mulki da kwanciyar hankali, da moriyar ci gabanta, wanda hakan martaba ce da ake nunawa dokokin kasa da kasa, da kuma huldar dake tsakanin kasashen duniya, kana martani ne ga aikin nuna fin karfi.  (Jamila)