logo

HAUSA

Sanarwar da Amurka da Japan suka fitar kan Sin almara ce kawai

2021-03-17 22:42:20 CRI

Sanarwar da Amurka da Japan suka fitar kan Sin almara ce kawai_fororder_1

A kwanakin baya, kasashen Amurka da Japan, sun kira taron manyan jami’ai a birnin Tokyo na Japan, amma abun mamaki shi ne, yayin taron, sun tattauna ne kan kasar Sin, kuma sanarwar da suka fitar bayan taron, an lura cewa, tana kunshe da aniyar Amurka, ta fadada adawa da kasar Sin, tare da kawancen Japan.

Daga gabashin teku zuwa kudancin teku, kuma daga tsibirin Diaoyu zuwa tsibirin Taiwan, haka kuma daga jihar Xinjiang zuwa yankin musamman na kasar Sin Hong Kong, kusan daukacin abubuwan da sassan biyu suka tattauna sun shafi kasar Sin ne, inda har suka ambaci sunan kasar Sin a cikin sanarwar, suna cewa, matakin kasar Sin bai dace da tsarin kasa da kasa ba. Ana iya cewa, sanarwar da suka fitar, shaida ce ta daban, da take nuna cewa, Amurka da Japan sun sake tsoma baki a cikin harkokin gidan kasar Sin.

Sanarwar da Amurka da Japan suka fitar kan Sin almara ce kawai_fororder_2

Hakika Japan ta riga ta samu babbar moriya daga cudanyar tattalin arzikin yankin Asiya, da hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya dake tsakaninta da kasar Sin, kuma abu mafi muhimmanci shi ne, sabuwar gwamnatin Amurka, ta fi mai da hankali kan moriyar kanta, don haka mai yiwuwa ne Japan ta yi babbar hasara, daga matakin da ta dauka tare da Amurka.

Ban da haka, yunkurin cacar baki da yin adawa da kasar Sin na Amurka da Japan, bai dace da bukatun al’ummun kasa da kasa ba, saboda ci gaban kasar Sin, zai samar da damammaki ga duk duniya, amma ba kalubale ba ne, idan Amurka da Japan ba su daina yin adawa da kasar Sin ba, sai dai lamarin zai kawo cikas ga ci gabansu, har ma ya haifar da matsala ga ci gaban shiyya shiyya. (Jamila)