Wasu kakanni mata da suka yi shahara a yanar gizo
2021-03-16 09:24:57 CRI
A birnin Quanzhou na kasar Sin, matan dake kauyen Xunpu sun shahara sosai a wurin, kuma suna da salon musamman na gyaran gashi da na kwalliya. Yawancinsu suna zaune ne a yankin Xunpu na gundumar Fengze dake birnin Quanzhou, wadanda kuma tushen su daga zuriy’ar Larabawa ne a zamanin da. Yanzu dai wasu kakanni mata dake kauyen Xunpu masu matsakaicin shekaru 70 sanye da kayan gargajiya suna rera waka, da rawa, da kuma gwaje-gwaje, sun shahara a yanar gizo. Gwaje-gwajen da suka yi irin na ‘yan kungiyar tsageru mata ne na wurin wanda aka yi a shekaru sama da goma da suka gabata. (Bilkisu)