logo

HAUSA

Gungun bangarori hudu ba zai cimma nasarar adawa da Sin ba

2021-03-16 20:53:54 CRI

Gungun bangarori hudu ba zai cimma nasarar adawa da Sin ba_fororder_1

A kwanakin baya ne shugabannin kasashe hudu, wato Amurka da Japan da Indiya da Australia, suka kira taron koli ta kafar bidiyo, wanda ya kasance taro na farko tun bayan da suka kafa gungun bangarori hudu. Duk da cewa, sanarwar da aka fitar bayan taron ba ta ambaci kasar Sin ba, amma abubuwan da suka bayyana a cikin sanarwar sun nuna cewa, suna adawa ne da kasar Sin.

Gidan rediyon NPR dake Amurka, shi ma ya bayyana cewa, kasashen hudu sun kira taron ne, domin Amurka na karfafa kawancenta na masu adawa da kasar Sin.

Alal misali, abubuwan dake cikin sanarwar suna kumshe da fannonin kandagarkin cutar COVID-19, da dakile sauyin yanayi, da matsalar tsaro a shiyya shiyya da sauransu, kuma Amurka da Japan da Australia, sun cimma matsaya guda, cewa za su kara zuba jari a kamfanonin hada magunguna na Indiya, domin a kara samar da allurar rigakafin COVID-19 a kasar.

Gungun bangarori hudu ba zai cimma nasarar adawa da Sin ba_fororder_2

Hakika dai ana ganin cewa, gungun bangarori hudu kamar wasan siyasa ne, wanda ba zai yiwu kasashen hudu su iya cimma nasarar yunkurinsu na yin adawa da kasar Sin ba.

Da farko, kasashen hudu, suna da manufofin siyasa mabanbanta. Misali, Amurka da Japan, sun fi mai da hankali kan kudancin teku da gabashin tekun kasar Sin, yayin da Australia ta fi mai da hankali kan yammacin tekun Pasifik. Sai kuma Indiya, wadda ta fi ba da muhimmanci kan tekun Indiya. A don haka, abu ne mai wahala Amurka ta cimma yunkurinta na adawa da kasar Sin, tare da sauran kasashen uku.

Na biyu kuma, kasashen Japan da Australia da Indiya, ba za su amince da matakin da Amurka za ta dauka ba, sakamakon moriyar tattalin arziki, duba da cewa a yanzu haka, kasar Sin ce abokiyar cinikayya mafi girma gare su, don haka ko shakka babu, ba za su so su rasa babbar kasuwar kasar ta Sin ba.

Alal hakika, ya dace kasashen duniya su tattauna kan harkokin kasa da kasa, domin daidaita matsalolin da suke fuskantar, kuma gungun bangarori hudu dake karkashin jagorancin Amurka, ba zai cimma yunkurinsa ba. (Jamila)