logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi hangen nesa wajen tunawa da jami’an wanzar da zaman lafiya yayin da take bada gudunmuwar riga kafi

2021-03-16 18:26:56 CRI

Kasar Sin ta yi hangen nesa wajen tunawa da jami’an wanzar da zaman lafiya yayin da take bada gudunmuwar riga kafi_fororder_0316-1

Shekara guda bayan barkewar cutar COVID-19 a duniya, kasashe yanzu sun zage damtse a kokarinsu na ganin bayanta, inda suke ta fafutukar samarwa ko neman alluran riga kafin da ya ba al’ummar duniya fatan ganin bayan cutar.

Sai dai yayin da aka dukufa a wannan fafutuka na samar da riga kafi, bai kamata a manta da jami’an wanzar da zaman lafiya dake aiki ba dare ba rana domin tabbatar da kwanciyar hankalin duniya ba.

A jiya ne zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya sanar wa sakatare Janar na MDD niyyar kasarsa ta bada gudunmawar alluran riga kafin COVID-19 dubu 300 ga jami’an wanzar da zaman lafiya na MDD dake aiki a kasashe daban-daban a fadin duniya. Hakika wannan ya kara nuna girma da hangen nesa da a kullum kasar Sin ke nunawa. Yayin da kasashe suka dukafa yi wa al’ummominsu riga kafin, an manta da mutane masu muhimmanci, wato jami’an wanzar da zaman lafiya.

Zuwa ranar 30 ga watan Yunin 2019, Majalisar Dinkin Duniya na da jami’an wanzar da zaman lafiya 100,411 dake aiki a kasashen nahiyoyi daban-daban. Daga cikin 86,145 jami’an tsaro masu kayan sarki, 12,932 kuma fararen hula, yayin da 1,334 suka kasance masu aikin sa kai.

Jami’an wanzar da zaman lafiya na bada kariya ne ga fararen hula, da kokarin rage aukuwar rikice-rikice da karfafa tsaro da inganta karfin kasashe na sauke nauyin dake wuyansu. Baya ga haka, suna taka rawa wajen bunkasa karfin kasashe na jurewa rikice-rikice da shimfida tubulin wanzar da zaman lafiya mai dorewa ta hanyar gano tushen tashe-tashen hankula.

Irin gudunmawar da suke bayarwa wajen tabbatar da kwanciyar hankalin gwamnatoci da al’ummominsu, da sadaukarwar da suke yi yayin da suke ci gaba da fuskantar kalubale, abu ne da ba zai taba misaltuwa ba. Ya kamata wannan yunkuri na kasar Sin, ya tunatar da sauran kasashe masu karfin tattalin arziki abun da ya kamata su yi, wato tallafawa wadannan mutane marasa rinjaye da suke sadaukar da jin dadinsu domin kwanciyar hankalin dimbin al’umma. Ya kamata a rika ba duk wani batu da ya shafi kare lafiyarsu da hakkokinsu tare da martabarsu muhimmanci, bisa la’akari da rawar da suke takawa. (Faeza Mustapha)