logo

HAUSA

Wasu ‘yan siyasar kasashen yamma sun nuna halin rashin kyautawa yayin bayyana halin da ake ciki a jihar Xinjiang

2021-03-15 19:51:59 CRI

Wasu ‘yan siyasar kasashen yamma sun nuna halin rashin kyautawa yayin bayyana halin da ake ciki a jihar Xinjiang_fororder_1

A kwanakin baya ne aka tilastawa wani shahararren shaihun malami dan kasar Faransa Christian Mestre, yin murabus daga aikinsa, saboda ya fadi gaskiya, bayan da ya kai ziyara yankin Xinjiang, shekaru biyu da suka gabata.

Kafin wannan, ‘dan jarida dake aiki a mujallar Le Point ta Faransa, Jérémy André Florès, wanda bai taba zuwa yankin Xinjiang ba, ya wallafa wani rahoto, inda ya bayyana cewa, zai tono kalaman da shaihun malami Mestre ya yi, domin nuna goyon baya ga kasar Sin. A sanadin haka, wasu rukunonin ‘yan adawa da kasar Sin dake Faransa, sun zargi Mestre, tare da matsa masa lamba da ya yi murabus daga mukaminsa, na jami’in kula da da’a, a wani aikin hadin gwiwar biranen kasashen Turai da ake gudanarwa a birnin Strasbourg.

Abun da ya fi jawo hankalin jama’a shi ne, masu gudanar da wancan aiki suna tattaunawa ne kan ko za a yarda da shigar da fasahar 5G wadda kamfanin sadarwa na kasar Sin Huawei ke fatan aiwatarwa a birnin na Strasbourg ko a’a.

Game da hakan, ‘dan jarida Jérémy André Florès, ya bayyana a fili a dandalin sada zumuntarsa cewa, wannan lamari dalili ne, da ya sa ya sake ambato lamarin da ya faru kafin shekaru biyu da suka gabata.

Wasu ‘yan siyasar kasashen yamma sun nuna halin rashin kyautawa yayin bayyana halin da ake ciki a jihar Xinjiang_fororder_2

A bayyane take, an lura cewa sun dauki matakin ne domin cimma burin siyasa, inda wasu ‘yan siyasa da kafofin watsa labarai na kasashen yamma, suke son bata sunan kasar Sin, bisa fakewa da yankin Xinjiang na kasar. Ba ma kawai ta hanyar baza jita-jita marasa tushe ba, har ma da daukar matakan zaluncin siyasa, kan mutanen da suka fada gaskiya.

Alal misali, an kira shafin yanar gizon Grayzone na Amurka, wanda ya tono jita-jitar kisan kare dangi, da masanin nan mai adawa da kasar Sin  Adrian Zenz ya samar, da sunan “mai adawa da manufar kisan kare dangi”, kuma an goge rahoton zargin jita-jitar Adrian Zenz, da shahararren masanin batun Syria na Amurka Joshua Landis ya ruwaito, a dandalin sada zumunta cikin sauri, wanda hakan ya sa Adrian Zenz ya ce zai kai kara.

Duk da cewa, wasu ‘yan siyasar kasashen yamma, suna shafawa yankin Xinjiang na kasar Sin bakin fenti ta hanyoyi daban daban, amma ko shakka babu, ba za su cimma burin yunkurinsu ba, saboda ci gaban Xinjiang zai jure jarrabawar lokaci da tarihi. (Jamila)