logo

HAUSA

Babban jami’in al’ummar Palasdinu: Nasarorin kasar Sin sun jawo hankalin duniya

2021-03-15 14:26:00 CRI

Bana jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin take cika shekaru 100 da kafuwa, kana shekarar farko ta shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 14, kuma manyan taruka biyu da aka kammala gudanarwa a kwanan nan, wato taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar NPC da na majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar CPPCC, sun jawo hankalin kasa da kasa sosai. Wakiliyarmu ta zanta da Ahmed Majdalani, memban kwamitin zartaswa na kungiyar ‘yantar da al’ummar Palasdinu, kana babban sakataren rundunar gwagwarmayar kwato ‘yancin Palasdinawa, kuma ministan kula da walwalar jama’ar, inda ya taya kasar Sin murnar kammala tarukan biyu lami-lafiya, tare da jinjina mata saboda dimbin nasarorin da ta samu a fannonin dakile cutar COVID-19, da yaki da fatara da kuma habaka tattalin arziki.

Ahmed Majdalani ya bayyana cewa, ya maida hakali sosai kan tarukan biyu na bana, musamman wasu sabbin manufofin da aka bullo da su game da kyautata rayuwar al’ummar kasar Sin, inda a cewarsa, nasarorin da kasar ta samu a fannoni daban-daban sun jawo hankalinsa sosai:

“Taron da ya shafi shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 14, ya tattauna kan wasu sabbin dabaru na aiwatar da ka’idoji, a wani mataki na bunkasa zamantakewar al’umma, da kara baiwa al’umma damar samun kudin shiga, da fadada tsarin demokuradiyya, tare kuma da kara shigar da mutane cikin tsarin inshorar tsoffi. A ganina, tarukan biyu na kasar Sin na bana sun fito da wasu muhimman batutuwa biyu, wato idan ana mayar da hankali kan raya tattalin ariki a cikin gida, za a iya hade kasuwar cikin gida da ta ketare domin samun ci gaba mai karfi da dorewa. A wani bangaren, ya kamata a tsaya ga raya kasuwar cikin gida, har ma kasar Sin ta cimma nasarar fitar da mutane masu fama da talauci a yankunan karkara da yawansu ya zarce miliyan 98 daga zaman talauci, al’amarin da zai taimaka sosai ga ci gaban tattalin arzikin kasa. A dayan bangaren kuma, zurfafa bude kofa ga kasashen waje a bangarori daban-daban zai taimakawa kasar Sin fadada kasuwarta a duk duniya, ba kasuwar cikin gida kawai ba. Har wa yau, wani abu na daban da ya jawo hankalina shi ne, maida batun yin kirkire-kirkire a matsayin tushe na aiwatar da shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 14, a nan kuma nake ganin yin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha zai taka muhimmiyar rawa a fannin zamanantar da kasar Sin, har ma kasar Sin tana matukar maida hankali kan kiyaye muhallin halittu da bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba. Shi ya sa tarukan biyu za su taimaka ga raya kasar Sin har ta zama kasa mai tsarin gurguzu irin ta zamani.”

Ahmed Majdalani yana kuma da yakinin cewa, bisa tushen cimma nasarar aiwatar da shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 13, gwamnati gami da al’ummar kasar Sin za su samu nasarar cimma muradun da aka tsara a irin wannan shiri na 14, inda ya ce:

“A nawa ra’ayi, wannan shirin da gwamnatin kasar Sin ta tsara sa’annan aka zartas da shi a wajen tarukan biyu na bana, ya tsara buri mai dorewa a fannin raya tattalin arziki, da inganta kwarewar kasar a fannin raya tattalin arziki da kimiyya da fasaha. A yanzu haka kasar Sin na kokarin shiga wani sabon mataki na bunkasa harkokin kimiyya da fasaha, wadda ke taka muhimmiyar rawa a duk fadin duniya.”

Majdalani ya yi karin haske cewa, a bara, yaduwar cutar mashako ta COVID-19 ta haifar da babbar illa ga tattalin arzikin duniya, amma kasar Sin ta samu babbar nasarar dakile ta, har ta samu habakar tattalin arziki. Ban da haka, Sin na kan gaba a duk duniya, wajen nazari gami da samar da alluran riga-kafin cutar. Majdalani ya kuma godewa kasar Sin saboda tura kwararrun likitocin da ta yi zuwa Palasdinu don taimaka mata yaki da cutar:

“Ina jinjinawa gwamnatin kasar Sin saboda jajircewarta a fannin ganin bayan cutar. Gwamnatin Sin tana tsayawa tsayin daka wajen daukar duk wani matakin da ya wajaba don dakile yaduwar cutar, wadda ta bayar da babbar gudummawa ga aikin ganin bayan cutar a duk duniya. Haka kuma kasar Sin na daya daga cikin kasashen da suke kan gaba wajen samar da alluran riga-kafin cutar, gaskiya wannan ya cancanci yabo matuka. A bara, kasar Sin ta turo mana rukunin kwararrun likitoci don fadakar da mu game da dabarun kandagarkin cutar. Kwanan nan kuma, Sin ta sanar da baiwa al’ummar Palasdinawa kyautar alluran riga-kafin cutar, wadanda za su iso nan bada jimawa ba.”(Murtala Zhang)