logo

HAUSA

Kasashe da dama na goyon bayan Sin kan batun jihar Xinjiang

2021-03-14 21:39:08 CRI

A yayin zama na 46 na majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD, kasar Cuba ta gabatar da wani jawabi a madadin kasashe 64, inda ta yaba wa gwamnatin kasar Sin kan matsayin da take tsayawa na dora muhimmanci kan moriyar jama’a, da inganta cimma nasara a fannin kiyaye hakkin bil Adama, ta kuma jaddada cewa, jihar Xinjiang wani sashi ne na kasar Sin da ba za a iya raba shi ba, ta kuma yi kira ga dukkan bangarori masu ruwa da tsaki da su martaba manufar ka’idojin MDD, da daina amfani da irin wadannan batutuwa wajen tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin. Wannan ya nuna aniyar galibin kasashen duniya na yin adawa da siyasantar da batutuwan dake shafar hakkin bil Adama.

A lokuta daban daban, wasu kasashe suna ta haifar da karairayi kan batutuwan da suka shafi Xinjiang, da bata sunan kasar Sin kan kokarinta na yaki da ta'addanci da kawar da tsattsauran ra’ayi. Kasashe masu tasowa da yawa sun tsaya tsayin daka kan nuna adalci da gaskiya, har sun yi magana tare a lokuta daban-daban don nuna goyon baya ga matsayin kasar Sin da matakan da ta dauka kan batutuwan da suka shafi Xinjiang.

Batutuwan da suka shafi jihar Xinjiang ba batun kare hakkin bil Adama ba ne, asalinsa shi ne nuna adawa da ta’addanci, kawar da tsattsauran ra’ayi, da kuma nuna adawa da nuna wariya. Zargin da wasu kafofin watsa labaru da ’yan siyasar kasashen yammacin duniya suka yi wa kasar Sin na "kisan kare dangi", "gudanar da aiki ala tilas" da "zaluncin addini", hanya ce da su kan bi don cimma burinsu a fannin siyasa, da nufin lalata tsaro da kwanciyar hankali a jihar da kuma hana ci gaban kasar ta Sin.

Amma, karya ba za ta iya boye gaskiya ba. Ko da yaushe kasar Sin na aiki tukuru don inganta tattalin arziki da zamantakewar jihar Xinjiang, da kiyaye zaman lafiyar jama'a, da kare 'yancin bil Adama na dukkan kabilun da ke jihar.

A cikin shekaru 60 da suka gabata, jimillar tattalin arzikin jihar Xinjiang ya karu har sama da sau 200, kuma matsakaicin shekarun haihuwa na jama’ar jihar ya karu daga shekaru 30 zuwa 72. A cikin shekaru 40 da suka gabata, yawan ’yan kabilar Uyghur da ke Xinjiang ya karu daga miliyan 5.55 zuwa fiye da miliyan 12. Don haka, "Kisan kare dangi" ba zai yiyuwar faruwa a kasar Sin ba.

Jihar Xinjiang ta mayar da inganta samar da aikin yi a matsayin muhimmin aiki a fannin kyautata zaman rayuwar jama’a. Mutanen jihar Xinjiang, su ma Sinawa ne, suna da ikon neman aikin yi a ko’ina a duk fadin kasar Sin, ba wanda zai iya hana tafiyarsu a cikin kasar ba. Alkaluma sun nuna cewa, tun daga shekarar 2014, jimillar ma'aikatan jihar Xinjiang dubu 117 ke aiki ko kuma sun taba yin aiki a larduna daban daban dake kasar, wanda hakan ke tabbatar da cewa, babu wani abin da ake kira "gudanar da aiki ala tilas" a jihar ta Xinjiang.

Jihar Xinjiang tana aiwatar da manufar bin addini cikin ’yanci. Dukkan mazauna wurin suna da iko a fannonin siyasa, tattalin arziki, zamantakewa da al'adu da dai sauransu. Babu wata kungiya ko wani mutum da zai iya tsoma baki cikin duk wasu ayyukan addini na yau da kullun da masu bin addini ke gudanarwa a wuraren ayyukan addini da cikin gidajensu. Yaya ake magana game da "zaluncin addini"?

Babu wanda ya fi gwamnatin kasar Sin wajen kulawa da hakkin bil Adama na Sinawa. Gwamnatin kasar tana matukar adawa da bata sunanta da wasu suka yi mata don dalilin siyasa. Ana fatan cewa, wasu kasashen yammacin duniya za su tinkara da warware matsalolinsu na hakkin bil Adama na kansu, kuma su daina tsoma baki a harkokin cikin gidan wasu kasashen ta hanyar amfani da batutuwan da suka shafi hakkin bil Adama, domin samun moriyarsu ta fuskar siyasa. (Bilkisu Xin)