logo

HAUSA

An Ba Da Amsa Kan Dalilin Da Ya Sa Gwamnatin Kasar Sin Ta Samu Amincewa Sosai

2021-03-13 17:30:25 cri

An Ba Da Amsa Kan Dalilin Da Ya Sa Gwamnatin Kasar Sin Ta Samu Amincewa Sosai_fororder_微信图片_20210313173229

A ‘yan shekarun da suka gabata, jerin binciken ra’ayin jama’a da cibiyoyin kasa da kasa suka yi, sun nuna cewa, kason Sinawa dake goyon bayan gwamnatinsu ya kai matsayin farko a duniya. To, ko mene ne dalilin? Sakwannin da firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayar a yayin taron manema labaru da aka shirya a ranar 11 ga wata, bayan rufe manyan tarukan biyu, wato taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa (CPPCC), da na majalisar wakilan jama’ar kasar (NPC), sun bude wata taga ga kasashen duniya don kara fahimtar wannan dalili.

Daga cikin sakonnin akwai, “Samar da aikin yi tubali ne na zaman rayuwar jama’a, kuma tushe ne na samun ci gaba”, “Kamata ya yi gwamnati ta zuba kudi a fannin kyautata zaman rayuwar jama’a, musamman ma ta fuskokin ba da ilmin tilas da hidimar jinya” da dai sauransu……

Wadannan batutuwan sun shafi rayuwar kowa da kowa. Harkokin jama’a na da muhimmanci gaya, kamar dai yadda sakon da aka fitar a bayyane a taron manema labarum yake,--"Babban burin neman ci gaban kasar Sin shi ne, bai wa Sinawa damar zaman rayuwa mai kyau."

A wannan rana kuma, hukumar kolin kasar dake tsara dokoki ta zartas da shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 14, da burin da ake fatan cimmawa nan da shekara ta 2035. An kuma gabatar da muhimman muradu 20 da za a cimma a shekaru biyar masu zuwa, inda guda bakwai suka shafi zaman rayuwar jama’a, adadin da ya wuce kashi daya cikin uku.

Daga sanya rayuwar mutane da lafiyarsu a gaba a yayin da ake fuskantar matsalar kiwon lafiyar jama’a, zuwa sanya batun samar da aikin yi a gaban komai lokacin da ake kokarin farfado da tattalin arziki, har zuwa bada muhimmanci ga inganta rayuwar jama’a a yayin da aka tsara shirin raya kasa na nan gaba, a ko da yaushe, gwamnatin Sin na martaba manufar bada muhimmanci ga harkokin jama’a yayin da take gudanar da ayyukanta, wato tana kokarin yin duk abubuwan da jama’ar kasar ke bukata. Wannan ne kuma babban dalilin da ya sa gwamnatin kasar Sin ta samu amincewa sosai na tsawon lokaci. (Mai fassara: Bilkisu Xin)