logo

HAUSA

Kwalliya ta biya kudin sabulu wajen raya harkokin diflomasiyya tsakanin Sin da Afirka

2021-03-13 21:27:11 CRI

Kwalliya ta biya kudin sabulu wajen raya harkokin diflomasiyya tsakanin Sin da Afirka_fororder_2

Jiya Jumma’a ne, cibiyar nazarin batutuwan kasa da kasa ta kasar Sin ta kaddamar da takardar bayani kan halin da duniya take ciki gami da harkokin diflomasiyyar kasar Sin tsakanin shekarun 2020 da 2021. Wallafa irin wannan takardar bayanin a kowace shekara, al’ada ce ta cibiyar, wadda ta fara aikin rubuta shi tun daga shekara ta 2006, tare da nufin yin nazari da kara fadakar da al’umma kan halin da duniya take ciki, da yadda kasar Sin ta gudanar da harkokinta a fannin diflomasiyya.

A wannan karon, bayanin ya takaita ayyukan diflomasiyyar da gwamnatin kasar Sin ta yi a shekara ta 2020, inda a cewarsa, a yayin da duk duniya ke fama da yaduwar cutar mashako ta COVID-19, kasar ta bullo da wasu sabbin dabarun diflomasiyya, da inganta mu’amala tsakanin shugabannin kasa da kasa, don kare muradunta da bada gudummawar shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk fadin duniya baki daya.

Kamar yadda takardar bayanin ta ce, shekarar da ta gabata, shekara ce ta musamman, saboda kasa da kasa sun fuskanci babbar barazana daga cutar COVID-19, matsalar da ta haifar da koma-bayan tattalin arziki da tawayar harkokin kasuwanci, gami da jawo rashin guraban ayyukan yi a kasashe daban-daban. Kasashe masu tasowa, ciki har da kasashen Afirka, sun fi jin radadin a jikinsu sakamakon yaduwar cutar.

Kwalliya ta biya kudin sabulu wajen raya harkokin diflomasiyya tsakanin Sin da Afirka_fororder_1

A daidai wannan lokaci, kasar Sin ta tashi tsaye don samar da alluran riga-kafin da ta kirkiro ga kasashe daban-daban, musamman kasashen Afirka dake da matukar bukata. Alkaluman da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya fitar kwanan nan, sun nuna cewa, kawo yanzu, kasarsa ta samar da kayan yaki da cutar na gaggawa ga Afirka har sau 120, da kuma samar da alluran riga-kafin cutar ga kasashe 35 dake nahiyar gami da kungiyar tarayyar Afrika wato AU.

Duk wadannan abubuwa sun zama kwararan shaidun dake nuna irin kyakkyawan zumunci da alaka tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, kuma hadin-gwiwar bangarorin biyu ya zama abun misali ga hadin-gwiwar da ake yi tsakanin kasashe masu tasowa gami da hadin-gwiwar sauran kasashe da Afirka.

A takardar bayanin, an kuma bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da fadada bude kofarta ga kasashen waje da neman samun moriyar juna, musamman a fannin ganin bayan yaduwar cutar, da habaka hadin-gwiwa da mu’amala tare da kasashe masu tasowa, musamman kasashen Afirka, don neman cimma burinta dake cewa “harkokin diflomasiyya za su biya bukatun al’umma”.

A bana, za’a gudanar da sabon taron dandalin tattauna hadin-gwiwar Sin da Afirka wato taron FOCAC a kasar Senegal, kuma muna fatan amfani da wannan dama don ci gaba da kyautata dangantakar zumunci tsakanin bangarorin biyu, musamman a fannin dakile cutar, da raya tattalin arziki da kasuwanci da kuma bunkasa ci gaban masana’antu da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.(Murtala Zhang)