logo

HAUSA

Kyautata tsarin zaben Hong Kong zai ba da kariya matuka ga tsarin demokuradiyyar yankin

2021-03-13 17:06:38 CRI

Kyautata tsarin zaben Hong Kong zai ba da kariya matuka ga tsarin demokuradiyyar yankin_fororder_微信图片_20210313173240

Bayan hukumar kolin kasar Sin dake tsara dokoki ta zartas da kudurin kyautata tsarin zabe a yankin musamman na Hong Kong a ranar 11 ga wata, ‘yan siyasan kasashen yamma, ciki har da Amurka, sun fara bata sunan kasar Sin, inda suka bayyana matakin da Beijing ta dauka a matsayin “Farmaki kan tsarin demokuradiyya”, da kuma “kashe ikon Hong Kong na tafiyar da harkokinsa da kansa” da dai sauransu.

A zahiri, tun dawowar Hong Kong karkashin ikon kasar Sin, a ko da yaushe, gwamnatin tsakiya ta kasar kan goyi bayan yankin wajen raya tsarin demokuradiyya dake dacewa da hakikanin halin da yake ciki. Amma, wadancan masu adawa da gwamnatin kasar da tayar da rikici a yankin da magoya bayansu dake adawa da kasar Sin, suna amfani da kura-kuran dake cikin tsarin zaben, don shiga harkokin siyasar yankin, kuma su ne wadanda ke hanawa da illata ci gaban tsarin demokuradiyyar yankin na Hong Kong.

Duk tsarin demokuradiyya dake iya dacewa da halin yankin Hong Kong, da kiyaye moriyar al’ummar yankin gaba daya, da kai yankin ga samun wadata da zaman karko, da kuma samun goyon baya daga mazauna yankin, to ana iya cewa, tsari ne mai kyau. Sukar da wasu ‘yan siyasan kasashen yamma suke yi, ba shi da tushe ko kadan bare makama. (Mai fassara: Bilkisu Xi n)