logo

HAUSA

Sinawa suna yakar cutar COVID-19 da allurar rigakafi

2021-03-12 20:10:11 CRI

Sinawa suna yakar cutar COVID-19 da allurar rigakafi_fororder_微信图片_20210308150258

Yanzu a duniyarmu akwai mutane fiye da miliyan dari da suka kamu da cutar, kana yawan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon cutar ya kai fiye da miliyan 2. Ta la’akari da dimbin yawan mutanen da suka harbu da cutar, wannan annoba ba za ta daina yaduwa da kanta ba, dole ne mu yi amfani da magani don kawo karshen yaduwarta.

Saboda haka, allurar rigakafi tana taka muhimmiyar rawa a kokarin dakile cutar. Kana zuwa yanzu kasashe daban daban da hukumar lafiya ta duniya WHO suna hadin gwiwa da juna don samar da riga kafi tare da raba su tsakanin al'ummomi daban daban.

A yau za mu tattauna batun cutar COVID-19, musamman ma yadda ake kokarin dakile annobar ta hanyar yi wa jama'a allurar rigakafin cutar a nan kasar Sin.(Bello Wang/Saminu Alhassan)

Bello