logo

HAUSA

Kyautata Tsarin Zabe Na Hong Kong Zai Taimaka Wajen Kyautata Halin Da Yankin Ke Ciki

2021-03-12 21:51:51 CRI

Kyautata Tsarin Zabe Na Hong Kong Zai Taimaka Wajen Kyautata Halin Da Yankin Ke Ciki_fororder_微信图片_20210312213644

A yau ne, mahukuntan kasar Sin suka shirya taron manema labaru, inda aka yiwa kafofin watsa labaru na Sin da na kasashen ketare bayani, gameda kudurin kyautata tsarin zabe na yankin musamman na Hong Kong na kasar, wanda hukumar kolin kasar dake tsara dokoki, wato majalisar wakilan jama’ar kasar (NPC) ta zartas da shi. Jerin sakwannin da aka gabatar a yayin taron sun nuna cewa, kyautata tsarin zabe na Hong Kong zai amfanawa sassa daban daban.

Al’ummar yankin Hong Kong sun dade suna Allah wadai da abubuwan da masu adawa da gwamnatin kasar Sin da tayar da rikici a yankin suka yi na amfani da kura-kuran dake cikin tsarin zaben, don shiga harkokin siyasar yankin, har ma da illata tsaron kasa da ci gaban yankin na Hong Kong.

A sabili da haka, mazauna Hong Kong da gaske suna maraba da zartaswar wannan kudurin da majalisar NPC ta yi. A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, mazauna yankin da dama sun nuna bukatunsu na "Masu kishin kasa su gudanar da harkokin Hong Kong da nuna goyon baya ga kyautata tsarin zabe", inda suka sanya hannu ta kafofin yanar gizo da kuma a zahiri.

Kyautata Tsarin Zabe Na Hong Kong Zai Taimaka Wajen Kyautata Halin Da Yankin Ke Ciki_fororder_微信图片_20210312213652

Binciken ra’ayin jama’a da majalisar nazari ta Hong Kong ya nuna cewa, kimanin kaso 70 cikin dari na wadanda aka tambaya, sun bayyana goyon bayansu ga kudurin na kyautata tsarin zabe na Hong Kong. Wannan ya nuna cewa, an kafa tubali mai kyau a tsakanin al’ummar yankin game da manufofin gwamnatin kwamitin tsakiyar kasar Sin game da harkokin Hong Kong.

A matsayinsa na yankin dake da ‘yanci a fannin tattalin arziki a duniya, tabbatar da kwanciyar hankali da wadata a Hong Kong, ba kawai ya dace da moriyar kasar Sin ba, har ma ya dace da moriyar kasashen duniya. A shekarar da ta gabata, an aiwatar da dokar tsaron kasa ta Hong Kong, rahoton binciken da aka yi ya nuna cewa, idan aka kwatanta da watan Janairun na bana da watan Agustan na bara, na iya fahimtar cewa, yawancin masana’antun dake Hong Kong dake bayyana tabbaci game da yanayin kasuwanci na yankin ya karu sosai. (Bilkisu)