logo

HAUSA

An ba da tabbaci ga tsarin dimokuradiyya a yankin Hongkong na kasar Sin

2021-03-12 11:12:44 CRI

An ba da tabbaci ga tsarin dimokuradiyya a yankin Hongkong na kasar Sin_fororder_微信图片_20210312111034

Majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, ta zartas da kudurin kyautata tsarin zabe a yankin Hongkong, wanda babban taron majalisar ta gabatar. Wakilai sun yi tafi na tsawon lokaci, don nuna cikakken goyon bayansa, matakin da ya nuna cewa, kudurin ya samu karbuwa daga jama’a sosai, wanda zai ingiza tsarin dimokuradiyya dake dacewa da halin da yankin Hongkong ke ciki, da ba da tabbaci ga zaman rayuwar jama’ar yankin, ta yadda za su aiwatar da ikonsu na dimokuradiyya.

Rikice-rikice dake tashi a Hongkong sun nuna cewa, masu bore dake ihun “Dimokuradiyya” sun bata dimokuradiyyar wurin. Sun yi amfani da koma bayan tsarin zaba a yankin wajen lalata ayyukan hukumar kafa doka, da ta yankin, da kawo cikas ga aiwatarwar dokar ta hanyar magudin zabuka iri-iri, matakin da ya kawo babbar illa ga ikon dimokuradiyyar jama’ar yankin Hongkong.

Hongkong wani yanki ne na kasar Sin, don haka majalisar wakilan jama’ar kasar Sin tana da iko da nauyin kyautata tsarin zabe a fannin tsarin mulki a yankin, wanda zai ba masu kishin kasa damar gudanar da harkokin mulki a yankin na Hongkong, matakin da zai tabbatar da tsarin dimokuradiyya na yankin.

Bisa kudurin da aka gabatar, ana iya ganin niyyar da gwamnatin tsakiyar kasar Sin ta dauka, ta ba da tabbaci ga ingiza bunkasuwar tsarin dimokuradiyya a yankin Hongkong. Alal misali, kwamitin zabe na Hongkong ya zama tushe na tsarin zabe, bayan kyautatawa da kudurin ya yi masa, kana mambobinsa na kunshe da mutane 1500 dake wakiltar bangarori 5 na yankin Hongkong. Ban da wannan kuma, ya baiwa kwamitin zaben ikon zabar ‘yan majalisar dokoki, da gabatar da sunayen ‘yan takarar majalisar kafa dokoki, baya ga ikon gabatar da suna da zabar kantoman yankin, matakin dake da babbar ma’ana ga bunkasuwar tsarin dimokuradiyya.

Shekarun nan baya-baya, ‘yan aware da kuma masu tsattsauran ra’ayi na yankin Hongkong, sun yi kokarin zama mambobin majalisar kafa doka na yankin, ta hanyar amfani da gibin dake cikin tsarin zabe, abin da ya tsananta tabarbarewar yanayin siyasar yankin. Zabar mambobin majalisar daga bangarori daban-daban, bisa wani nagartaccen sabon tsari, zai kawar da tsattsauran ra’ayi a siyasance, da hana kwamitin fadawa hannun ‘yan aware, ta yadda za a tabbatar da bunkasuwar dimokuradiyya a mataki-mataki.

Kasashen duniya su kan kyautata tsarin zabe bisa halin da suke ciki, a matsayin hanyar da ta dace a kokarin raya tsarin dimokuradiyya. A hannu guda, wasu kasashen yamma dake tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin ciki hadda batun Hongkong, suna fakewa da batun dimokuradiyya, inda ba su so su waiwayi yanayin da ake ciki a lokacin mulkin mallaka da aka yi a Hongkong. A wancan lokaci gwamnatin kasar Birtaniya ta nada jagoran yankin ba tare da yin zabe ba, kuma mazauna yanki ba su da ikon yin zanga-zanga a kan tituna. Abun tambaya a nan shi ne, ko hakan dimokuradiyya ce?

Sabanin abun da ya faru a lokacin mulkin mallakar Birtaniya, bayan dawowar yanyin Hongkong kasar Sin, gwamnatin tsakiya ta nace ga raya tsarin dikokuradiyya a yankin bisa wasu nagartattun matakai, inda ta baiwa yankin ikon tafiyar da harkokinsa da kansa. Sa’an nan gyaran dokar da aka yi a wannan karo, ba shakka zai inganta zamantakewar mazauna Hongkong, da taimakawa yankin wajen bunkasa dikokuradiyyarsa.

Ana iya ganin cewa, kyautatawar da aka yi ga tsarin zabe bisa ka’idar “Baiwa masu kaunar kasa damar gudanar da mulkin Hongkong”, gwaji ne mai kyau da Sin take yi wajen kyautata tsarin zabe a wasu yankuna, bisa tushen tabbatar da ikon mulkinta. Kuma ya baiwa sauran kasashe fasahohi irin na kasar Sin, na aiwatar da dimokuradiyya a wasu yankuna, tare da tabbatar da ikon mulkin kasa gaba daya. (Amina Xu)