logo

HAUSA

Kwalliya ta biya kudin sabulu game da tarukan NPC da CPPCC

2021-03-11 20:39:09 CRI

Kwalliya ta biya kudin sabulu game da tarukan NPC da CPPCC_fororder_1

A ranekun 10 da 11 ga watan Maris din nan ne, aka rufe zama na hudu na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar Sin wato CPPCC karo na 13 da na majalisar wakilan jama’ar kasar, wato a takaice dai NPC.

Abubuwan da suka yi matukar jan hankali game da tarukan biyu na bana, su ne yadda suka gudana a kan lokacin da aka saba gudanar da su, wato cikin watan Maris ba tare da wata matsala ba. Kuma a bana, shugaban kasar Sin Xi Jinping, da sauran manyan jami’an kasar Sin sun halarci bikukuwan rufe tarukan na majalissar CPPCC da na NPC a birnin Beijing.

Gabanin kammala zaman majalissar ta CPPCC na bana, mambobin ta sun saurari muhimman jawabai game da ayyukan gwamnati, inda aka tattauna matuka, game da rawar da kasar Sin ta taka game da yaki da cutar COVID-19 da ta addabi duniya, tun bullar cutar, da matakan kandagarki, zuwa yadda take samar da rigakafi kyauta ga kasashe masu tasowa da dama, karkashin manufar ta ta sanya rigakafin ya zama wata haja ta dukkanin bil Adama.

Kaza lika, taron ya tabo batun kyakkyawar dangantakar dake wakana tsakanin Sin da kasashen Afirka, karkashin dandalin nan na FOCAC mai shekaru 20 da kafuwa.

Kwalliya ta biya kudin sabulu game da tarukan NPC da CPPCC_fororder_2

Har ila yau, an yi musayar yawu game da yanayin da ake ciki, game da  diflomasiyar Sin da Rasha, da Sin da Amurka. Sai kuma batun matsayar Sin don gane da yankin Hong Kong da Taiwan, da ma fatan ta na kare martabar ikon mulkin kai, da wanzuwar tsarin kasa daya salon mulki biyu na Hong kong, da kwaskwarima game da dokokin gudanarwar yankin na Hong Kong, tare da jaddada kira ga masu sukar kasar Sin, don game da yadda take gudanar da jagorancin yankunan ta, ciki har da jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kan ta, da su kauracewa hakan.

A jimlace dai muna iya cewa, Sin ta gudanar da wadannan muhimman taruka na bana, a wata gaba da duniya ke ci gaba da bukatuwa da gudummawar ta, a fannonin raya tattalin arziki da zamantakewa. Don haka masharhanta da dama ke ganin lokaci ya yi, da duniya za ta karfafa hadin gwiwa da Sin a dukkanin fannoni, domin ciyar da rayuwar bil adama gaba.

Sanin kowa ne dai, shugabannin sassan duniya da dama, da masana da masu fashin baki, wadanda suka yi tsokaci game da tarukan NPC da CPPCC, tuni suka jinjinawa taron, musamman duba da yadda Sin ta cimma nasarar kakkabe matsanancin talauci tsakanin al’ummar ta, tun gabanin manyan tarukan na bana. Don haka a iya cewa “Kwalliya ta biya kudin sabulu”, don gane da kwazon JKS, da gwamni da al’ummar Sinawa, game da ciyar da kasar su gaba, da ma gudummawar da hakan ke baiwa ci gaban rayuwar bil Adama baki daya. (Saminu Hassan)