logo

HAUSA

Ikon fadin albarkacin baki a yammacin duniya yana cikin wani mummunan yanayi

2021-03-11 17:57:58 CRI

Ikon fadin albarkacin baki a yammacin duniya yana cikin wani mummunan yanayi_fororder_1

Shekaru biyu da suka gabata, farfesa Christian Meistre dake koyarwa a jami’ar Strasbourg ta kasar Faransa ya ziyarci jihar Xinjiang dake kasar Sin, inda ya ganewa idanun sa yanayin da cibiyar horas da sana’o’i, da cibiyar karantar da addinin Musulunci dake jihar take gudanar da ayyukan ta, daga bisani kuma ya yi rubutu mai kunshe da jinjina ga kasar Sin, bisa sahihan matakai da take aiwatarwa na dakile yaduwar ta’addanci da kawar da tsattsauran ra’ayi. Marubucin, kuma shaihun malami, ya ma bayyana yadda a ganinsa ya kamata Faransa, da sauran kasashen yammacin duniya ya dace su fuskanci kalubalen ta’addanci bisa koyi daga kasar Sin.

Bugu da kari, shaihun malamin ya ce ya nazarci yadda rubuce-rubucen adabi na kasar Sin suka taimaka wajen habaka musayar ilimi tsakanin Faransa da Sin, sannan ya kuma yabawa matakan da Sin ta aiwatarwa a fannin kandagarkin yaduwar cutar numfashi ta COVID-19.

Sai dai fa a lokacin da ya yi wannan rubutu, ba wanda ke da masaniyar cewa, gaskiyar da ya bayyana game da Sin, da kaunar da ya nunawa Sin, za su sanya wani dan jarida na Faransa mai suna Jérémy André Florès ya soke shi, tare da rubuta wasu kalamai da suka tunzura wani gungu na Faransawa masu kyamar Sin, har ta kai su ga tursasa shaihun malamin ya yi ritaya daga aiki.

Wani abun tambaya ma game da wannan batu shi ne, me ya sa sai bayan shekaru 2 da wancan rubutu na farfesa Christian Meistre, dan jarida Jérémy André Florès ya bujiro da batun sukar farfesa Christian Meistre tsakanin kafofin watsa labarai ta Faransa dake kyamar Sin, da ma sauran ’yan siyasa masu ra’ayi daya da kafar?

Idan an yi kallo na tsanaki daga rubutun dan jarida Jérémy André Florès mai adawa da kasar Sin dake Faransa ya wallafa a shafinsa na Tiwita, za a ga cewa, bayanin da dan jaridar ya yi wanda ya tado da zancen sukar farfesan, yana da alaka ne ta kai tsaye da batun kamfanin Huawei na kasar Sin.

Dan jaridar mai kin jinin Sin ya ce yana fatan za a sallami farfesa Christian Meistre daga aiki, saboda baya ga kasancewar farfesan na aiki a jami’ar Strasbourg, a hannu guda kuma, yana aiki karkashin ofishin lura da da’ar aiki, wanda hukumar lura da birnin na Turai ke aiwatarwa, a kuma gabar da ake muhawar game da ko za a amincewa kamfanin Huawei na kasar damar yin aikin fasahar samar da 5G a birnin ko a’a.

Akwai alamun cewa, ko da ma farfesa Christian Meistre ba shi da wata alaka da kamfanin Huawei, makiyan kasar Sin na Turai da Amurka da suka sha alwashin kawar da kamfanin Huawei, ba za su yi kasa a gwiwa ba, wajen kawar da farfesan daga wannan mukami da yake kai, domin dai kawai su kai ga cimma burikansu na siyasa.

Don haka, karkashin manufofin makiyan Sin na yammacin duniya dake yayata karairayi game da manufofin da ake aiwatarwa a jihar Xinjiang,  karkashin inuwar wasu kudurori na kafofin watsa labarai na kasashen turai da Amurka game da jihar Xinjiang, dan jarida Jérémy André Florès, ya dauki ra’ayin farfesa Christian Meistre game da matakan dakile ta’addanci, da kawar da shi baki daya, wadanda ya gani da idanunsa a ziyararsa a jihar Xinjiang cikin watan Satumbar shekarar 2019, a matsayin damar kai masa hari, tare da bayyana shi a matsayin daya daga masana na Turai, wadanda akidun Sin suka ratsawa zuciyar su, yana mai cewa, wannan dan barandar Sin ba zai taba ci gaba da kasancewa mamba a hukuma mai muhimmanci dake birnin na Strasbourg ba.

Bugu da kari, wancan dan jarida mai sukar Sin, ya soki farfesa Christian Meistre da laifin karfafa gwiwar fadada cudanyar ayyukan binciken ilimi tsakanin bangaren Sin da jami’ar Faransa ta Strasbourg inda yake koyarwa. Kana ya taba yin maraba da zuwan cibiyar Confucius da ta shiga makarantar, ya taba gayyatar jami’in ofishin jakadancin Sin dake Faransa ya gudanar da wasu ayyukan raya al’adun yankin Tibet a birnin, ya kuma jinjinawa matakan da Sin ta rika aiwatarwa lokacin yaki da cutar COVID-19, dalilan da dukkaninsu, dan jarida Jérémy André Florès ya yi amfani da su wajen sukar farfesa Christian Meistre.

Ikon fadin albarkacin baki a yammacin duniya yana cikin wani mummunan yanayi_fororder_3

Wani abun lura ma shi ne, yadda mahangar wannan dan jarida mai kin jinin Sin, a baya bayan nan ta sha suka daga masanan kimiyya, bisa hujjar cewa, ya sauya ra’ayin wasu kwararrun kasa da kasa a rubutunsa, bayan sun gabatar da nasu ra’ayi game da ziyarar da suka kai birnin Wuhan, a wani mataki na nazarin tushen cutar COVID-19. Da wannan muna iya fahimtar ko wane ne dan barandar wani bangare na siyasa, tsakanin farfesa Christian Meistre da dan jarida Jérémy André Florès.

Wani abun takaici shi ne, irin yadda wadancan gungu na masu kin jinin Sin daga dan jarida Jérémy André Florès da sauran jami’ai makiyan Sin, ba su tsaya kan sukar farfesa Christian Meistre ba, inda suka ci gaba da makirci na yunkurin tursasa farfesan ya sauya kalamansa, wai ya ce “Ba a fahimci kalamansa na baya game da jihar Xinjiang ba”.

Game da wannan batu, wakiliyarmu, ’yar jarida Bai Yunyi, da Xie Wenting, wadanda suka zanta da farfesan a Xinjiang a shekarar 2019, sun bayyana cewa, a ganin su farfesa Christian Meistre ya sha fuskantar matsin lamba daga gungun makiyan Sin dake Faransa, inda suka matsa masa lamba cewa ya sauya kalaman sa, ’yan jaridar sun fada masa abun da ya fada haka suka wallafa, bayan sun duba kalaman nasa na wadancan shekaru 2, kuma mafi yawa daga kalmomin da malamin ya fada sun tsamo su yadda suke daga maganganunsa na ainihi.

Ikon fadin albarkacin baki a yammacin duniya yana cikin wani mummunan yanayi_fororder_4

Ikon fadin albarkacin baki a yammacin duniya yana cikin wani mummunan yanayi_fororder_微信图片_20210311183524

Wadannan ’yan jarida sun kara da cewa, kalaman farfesar game da aiwatar da dabarun sauya tunanin wadanda suka taba shiga ayyukan ta’addanci da kandagarkin ta’addancin a Xinjiang, sun dace da gaskiya kuma suna da ma’ana. Farfesan ya gwada halin jihar da abun da ake fama da shi a Faransa, kuma hakan wani abun a yi nazari ni a kan sa.

Bai Yunyi ta ma ce a shekarun baya bayan nan, wasu masana na kasashen waje da ’yan siyasa kamar su farfesa Christian Meistre, dake da niyyar fadin gaskiya game da kasar Sin, suna shiga hali na dar dar, ko yarda kafofin watsa labaran Sin su zanta da su. Tana ganin yanayin fadin albarkacin baki game da Sin a kasashen Turai ba shi da kyau ko kadan.

Ga misali, ta ce wani tsohon jakada na wata kasa ya taba bayyana wannan yanayi da Turai ke ciki, amma sai wasu kafofin Turai suka bayyana shi a matsayin "Tongzhong" wato mai gudanar da wata kulla kulla da hadin gwiwar Sin.

Ko shakka babu, baya ga abun da farfesa Christian Meistre ya fuskanta a yanzu, a Amurka, da Australia, da Birtaniya da Canada, karin masana da yawa, ko da abun da suka fada gaskiya game Sin bai wuce kalma daya ko biyu ba, ko suka kulla wata huldar musayar ilimi da Sin, hakan na iya sanyawa a bayyana su a matsayin wadanda ba su da hangen nesa.

A Amurka, irin wadannan malamai ana iya cafke su, su fuskanci wasu matsin lamba ta fuskar siyasa. Hakan na iya kaiwa a yi musu kagen sharri da yi musu hukunci.

Bai kamata a ce managarcin ra’ayin jama’a yana da bangare ne guda daya ba, Halin da farfesa Christian Meistre ya fuskanta da ma wasu makamantansa, da kuma mummunan yanayin watsa labarai da wasu kafofin yammacin duniya suke ciki don gane da jihar Xinjiang ta kasar Sin, da ma sauran batutuwa masu nasaba da Sin, dukkaninsu na nunawa duniya cewa, ikon fadin albarkacin baki a yammacin duniya yana cikin wani mummunan yanayi. (Saminu Alhassan)