logo

HAUSA

Taruka biyu na kasar Sin sun bayyana ingantaccen salon demokuradiyyar kasar

2021-03-10 21:44:04 CRI

Taruka biyu na kasar Sin sun bayyana ingantaccen salon demokuradiyyar kasar_fororder_A

Taruka biyu, wato taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC, da na majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar CPPCC, tamkar alkibla ce ta manufofin kasar Sin dake jawo hankalin kasa da kasa, kana muhimmiyar dama ce ga kasashen duniya don su ganewa idanunsu yadda kasar take aiwatar da tsarin demokuradiyya. A yayin tarukan biyu na bana, wakilan jama’ar kasar Sin da yawansu ya tasam ma dubu 3 gami da membobin majalisar CPPCC sama da dubu 2 sun hallara a Beijing, inda suka tattauna kan wasu muhimman daftarori gami da shirye-shiryen da suka shafi ci gaban tattalin arziki da rayuwar al’ummar kasar Sin nan da shekaru 5 ko 15 masu zuwa, al’amarin da ya sake bayyana tsarin demokuradiyya mai inganci na kasar.

Wace irin demokuradiyya ce mai kyau? Shaidu sun nuna cewa, tsarin demokuradiyya, shi ne tsarin dake dacewa da hakikanin halin da ake ciki, wanda ya fi aminci da amfani.

Taruka biyu na kasar Sin sun bayyana ingantaccen salon demokuradiyyar kasar_fororder_B

Idan muka yi misali da wadannan tarukan biyu don nazarin siyasar demokuradiyyar kasar Sin, za mu iya gano cewa, siyasar demokuradiyya irin ta gurguzu kuma mai salon musamman na kasar Sin, tana taka rawa sosai wajen zamanantar da tsarin tafiyar da harkokin mulki a kasar.

Wakilai gami da membobin da suka wakilci miliyoyin al’ummun kasar Sin sun hada da jami’an gwamnati, da shugabannin kamfanoni, da mutane daga bangarorin kimiyya da fasaha da ilimi, da kuma ma’aikata da manoma daga kananan hukumomi, al’amarin da ya tabbatar da cewa, abubuwan da jama’a daga matakai daban-daban suka maida hankali a kai, za’a iya kai su wurin da ake tattaunawa wato wajen tarukan biyu, ta yadda za’a haifar da tasiri gami da taimakawa tsara manufofin kasar.

Ana mamakin yadda kasar Sin ta iya yin wasu abubuwan al’ajabi biyu, wato saurin ci gaban tattalin arziki gami da zaman lafiya mai dorewa, siyasar demokuradiyya ta gurguzu mai salon musamman ta kasar ta amsa daya daga cikin wadannan tambayoyi.(Murtala Zhang)