Tsokacin farfesa Sheriff Ghali Ibrahim kan muhimman taruka biyu na kasar Sin
2021-03-09 14:39:52 CRI
Farfesa Sheriff Ghali Ibrahim, darektan ma’aikatan horas da ‘yan majalisu ne na jami’ar Abuja, wanda kuma shi ne shahararren masanin harkokin kasar Sin a tarayyar Najeriya.
Kwanan nan, ya zanta da Murtala Zhang game da muhimman taruka biyu da har yanzu suke gudana a birnin Beijing na kasar Sin, wato taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar NPC, gami da na majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar CPPCC.
A cewar farfesan, tarukan biyu suna da matukar muhimmanci ga kasar Sin har ma ga duk duniya baki daya. Ganin yadda cutar mashako ta COVID-19 ke ci gaba da kawo illa ga tattalin arziki da rayuwar al’ummun kasashe daban-daban, sabon shirin raya kasa na shekaru biyar masu zuwa da kasar Sin ta bullo da shi a wajen taron, zai karfafa gwiwar kasar gami da duniya baki daya wajen taimakawa ci gaban tattalin arziki da kyautata rayuwar al’umma.
Farfesan ya kuma yi tsokaci kan sauran wasu muhimman batutuwan da aka tattauna a wajen tarukan biyu. (Murtala Zhang)