logo

HAUSA

Kara raya kasuwar kasar Sin zai kara samar da damammaki ga duniya

2021-03-09 22:07:35 CRI

Kara raya kasuwar kasar Sin zai kara samar da damammaki ga duniya_fororder_1

Tun daga watan Mayun bara har zuwa yanzu, shugabannin kasar Sin sun sha jaddada cewa, idan aka mayar da hankali kan raya tattalin ariki a cikin gida, za a iya hade kasuwar cikin gida da ta ketare domin samun ci gaba mai karfi da dorewa. Ana kara tattaunawa kan wannan batu a yayin muhimman taruka biyu na bana dake gudana a halin yanzu.

Amma har yanzu akwai damuwar dake nuna cewa, shin kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa kan bude kofarta ga kasashen waje ko a’a, shin raya kasuwar cikin gida zai haifar da matsin lamba ga masu zuba jarin waje   ko a’a? Bayyana irin wannan damuwa na nufin akwai rashin fahimta game da wannan manufa.

A cikin rahoton aikin gwamnatin da firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gabatar, an sake jaddada muhimmiyar manufar habaka bukatun cikin gida. Hakan na nufin cewa, kasar Sin za ta kara raya kasuwar cikin gida, da kara samar da wata kasuwar kasa da kasa ga duk duniya.

Kara raya kasuwar kasar Sin zai kara samar da damammaki ga duniya_fororder_2

Abun lura a nan shi ne, babu sabani a tsakanin raya kasuwar cikin gida da fadada bude kofa ga kasashen waje da kasar Sin take yi. Maimakon haka, suna taimakawa juna ne. A shekaru sama da 40 da suka gabata, kasar Sin ta ci gajiya sosai daga manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga kasashen waje, inda ta fahimci cewa, idan ana son samar da ci gaba mai inganci, ya zama dole a kara bude kofa ga kasashen ketare, da habaka dangantaka da mu’amalar tattalin arziki tare da sauran kasashe.

A wajen tarukan biyu da ake gudanarwa a halin yanzu, a cikin rahoton aikin gwamnati gami da shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 14, gami da burin da ake fatan cimmawa nan da shekarar 2035, kalmomin “bude kofa” sun bayyana sau da dama. Kasar Sin tana bude kofarta har ma za ta ci gaba da bude kofarta ga kasashen waje, kuma ba za ta daina ba har abada.(Murtala Zhang)