logo

HAUSA

Gasar hunturu ta birnin Beijing ta haifar da fadadar harkokin wasanni

2021-03-09 09:34:56 CRI

Gasar hunturu ta birnin Beijing ta haifar da fadadar harkokin wasanni_fororder_1

Yayin gwajin wasannin da za a gudanar a lokacin gasar Olympics ta lokacin hunturu da birnin Beijing ke shirin karbar bakunci a badi, an shaida yadda dan wasa na farko ya yi tsalle cikin filin wasan zamiyar kankara na kasa, wanda hakan ya alamta fara gwajin wasanni a filin, lamarin da ya sanya wasu daga jami’an dake lura da ayyukan shirya gasar a filin zubar da hawaye.

Hakika ayyukan da aka gudanar ba masu sauki ba ne. Bayan tattaunawa da zantawa da dukkanin masu ruwa da tsaki, shirin gwaji mai lakabin  "Meet in Beijing" wato “mu hadu a Beijing” da a baya aka yi ta dagawa saboda barkewar annoba, a yanzu an gudanar da shi, a lokacin dusar kankara na karshe kafin bude gasar Olympics din ta birnin Beijing.

A tsakiya zuwa karshen watan Fabarairu, an gudanar da gwaje gwajen wasannin dusar kankara, da na zamiyar kankara daban daban. Daga ranekun 16 zuwa 26 ga watan, an gudanar da gwajin wasanni 20 a wuraren gudanar wasanni 3 dake Zhangjiakou, da Yanqing. A lokacin an gayyaci ‘yan wasa na gida, da kwararru a fannin wasannin hunturu na gida, don su shiga tare da tantance dukkanin kayayyakin da aka tanada domin gasar, ta yadda za ta tabbatar da yanayin gudanarwa, da kuma na ba da hidima, yayin da ake gudanar da wasanni. A lokacin ne kuma aka kaddamar da ayyukan helkwatar gasar mai lakabin "Winter Olympic Brain" wato kwakwalwar gasar Olympic ta lokacin hunturu.

Yayin da ya rage kasa da shekara guda a bude gasar, irin wadannan gwaje gwaje na da matukar muhimmanci, za su kuma samarwa kwamitin shirya gasar wasu damammaki na gano dabaru, da kwarewar cimma nasara.

A babban yankin wasannin kankara na Yanqing, an gudanar da ayyuka karon farko bayan kammala shi. Ana sa ran gudanar da karin wasu wasanni kanana 10 cikin kwanaki 10. Wadannan ayyuka za su shafi amfani da kayan wasan kankara da ake bukata yayin gasar ta Olympics ta lokacin hunturu.

Duk da cewa an rage yawan gwaje gwajen da aka tsara aiwatarwa, wuraren gudanar da gasar, da matakan dakile annoba, da ayyukan da aka tsara domin cimma nasarar gudanar da ita yadda ya kamata, ba su sauya ba.

Yayin gudanar da gwajin, helkwatar dake Shougang ta kwamitin tsara gasar dake birnin Beijing ta kaddamar da aikin ta. A cibiyar akwai manyan allunan kwamfuta 4 dake hade wuraren gudanar da gasar, akwai kuma wasu hukumomi 8 da za su lura da harkokin kasuwanci. Ofishin ya kuma tsara ayyukan samar da tabbaci ga hada hadar da ta shafi biranen gasar. Helkwatar dai za ta kasance babbar cibiya ta lura da dukkanin harkokin gasar ta Olympics dake tafe.

Da yake tsokaci game da hakan, daraktan sashen lura da ayyuka na kwamitin shirya gasar ta Olympics ta lokacin hunturu da birnin Beijing  zai karbi bakunci Mr. Yao Hui, ya ce yayin da ake aiwatar da harkokin gwaji, helkwatar na gudanar da tsara ayyuka a wuraren wasanni, ita ce kuma wurin tuntuba da watsa bayanai.

Kaza lika helkwatar na kunshe da kwamitin tsara wasannin musamman. An dai tsara gudanar da wasannin nuna kwarewar wasannin zamiyar kankara na “freestyle skiing” da na “snow skills” da na “aerial skills” a cibiyar wasanni ta “Yunding” bayan sauyawar yanayin bugawar iska, da sauyin yanayin zafi, wanda bai dace da gasar a sauran yankunan ba.

Shi kuwa babban sakataren gudanarwa na yankunan wasannin kankara a gundumar Zhangjiakou dake Yunding Ma Xuan, cewa yayi, dukkanin ayyukan da za a gudanar suna da alaka ne da tsare tsaren da aka aiwatar, Ko da yake akwai wasu abubuwa da ka iya bullowa ba zato, ko sauyin wuraren gudanar da wasu gasanni. A irin wannan yanayi ana sa ran masu kula da filayen wasanni za su yi aikin su. A fannin kandagarki da shawo kan annoba kuwa, akwai ayyukan yin gwajin lafiya masu nasaba da wasanni. Ko da ma masu daukar rahotanni an tsara musu yadda za su yi nesa da sauran mutane zuwa sama da mita 2, yayin da suke zantawa da masu wasan motsa jiki.

Jami’in ya ce, za a yi amfani da dukkanin matakan kandagarki na yaki da annobar COVID-19, kuma zai kasance abu mai sauki idan an kiyaye kusantar juna.

Daya daga wadanda suka taba aikin zantawa da ‘yan wasa a wuraren gudanar da gasannin hunturu, kuma wanda ya rike mukamin jagoran tsare tsaren intabiyu, karkashin hukumar kasa da kasa ta wasannin kankara Joe Fitzgerald, ya ce da yawa daga jami’ai masu kwarewa a wannan fanni sun gamsu da shirin gwajin lafiya da aka tsara gudanarwa a wuraren gudanar da gasar dake tafe.

Mr. Nomonds Cotans, kwararre a fannin gasar kankara, shi ma ya bayyana cewa, idan an kalli lamarin ta wani bangaren, cibiyar lura da na’urorin wasan kankara, ita ce wadda aka fi ziyarta da kuma samun kulawa.

Ya ce "Wurin na da kyau sosai a bangaren gini da kuma samar da kayayyakin da ake bukata. An yi hangen nesa sosai wajen ginin cibiyar, an kuma samar da kayan aiki masu inganci. Ina ga duk wanda ya zo wannan wuri zai ji dadi sosai".

A dukkanin wuraren gasannin, an tanadi tsarin aikin kiwon lafiya mai kunshe da kwararru a fannin wasannin kankara, ta yadda idan ‘yan wasa sun gamu da tsautsayi na jin ciwo, za su iya samun kulawa cikin gaggawa.

Zhang Huiliang, likita ne dake da shekarun aiki a wannan fanni har na tsawon shekaru 10, an zabe shi domin ya shiga tawagar masu lura da ‘yan wasan Olympics na hunturu a lokacin gasar. A ra’ayin Zhang Huiliang, babban kalubalen da ake fuskanta shi ne, santsi da kuma tudu da kwari. Kasancewar dole ne a daidaita yanayin jikin wanda za a duba lafiyarsa. Domin wasu yanayi kamar na kula da rauni a kai, an tanaji kwararru da za su ba da jiyya a kan lokaci.

Bai Bai, mamba ne na tawagar kwararrun likitoci da za su yi aiki a cibiyar wasannin zamiyar kankara ta “Alpine Ski” ya ce "Yanzu haka muna iya cewa muna da ikon kammala aikin kare lafiya, ta ‘yan wasan gida dake wannan cibiya ta “alpine skiing”, kuma muna da karfin gwiwar yin irin hakan yayin wasannin gasar Olympics dake tafe a badi".

Da yawa daga jami’an cibiyar tsallen kankara ta “Ski Jumping Center” na ganin aiki tukuru da aka yi cikin watanni sama da 3, sun haifar da sakamako mai gamsarwa.

A tsokacin sa, Mu Yong, wanda shi ne mataimakin daraktan cibiyar ta “Ski Jumping” na ganin sun gamu da wahalhalu masu tarin yawa, ciki har da na hada ayyukan sassa daban daban, da sauya abubuwan da aka bukata a wurin gudanar da wasu wasanni. Mu na ganin wadannan watanni 3 cike suke da wahalhalu da shan aiki ga dukkanin jami’ai.

Shi kuwa Dirk Schumann, kwararre a fannin sauyawa wurare fasali don gudanar da bajimtar gangarowa a kan su, cewa ya yi, yana matukar farin ciki da ganin an shafe tsawon lokaci ana shiri, komai ya zo karshe yadda ake fata, sai kawai jiran shekara mai zuwa, lokacin da za a gudanar da gasar Olympics ta birnin Beijing. Ya ce “Mun gudanar da shirye shirye bisa tsari, kuma kasancewar kwararru a fannin kiwon lafiya a wurin, ya sa mun yi aiki cikin nutsuwa da cikakkiyar kariya."

Wani kwararren a fannin tsara wuraren gudanar da wasannin kankara David Cerato, ya ce "Ayyukan gwaji, su ne kashin bayan cimma nasarar gasar. Ya ce “A gani na ayyukan gwaji da aka gudanar, sun haifar da nasara a fannin tsara gasanni da za a gudanar cikin tsauni”.

Dukkanin bangarorin masu ruwa da tsaki sun shaida cewa, za a yi gwaji sau 10 a watannin Oktoba da Disamba. Za a yi gwajin ne kan dukkanin fannoni cikakku, kana za a gabatarwa hukumomi daban daban, kamar kwamitin kasa da kasa na shirya gasar Olympic, da ‘yan wasan motsa jiki daga kasashe daban daban, da tawagogin watsa shirye shiryen talabijin, gayyatar shiga ayyukan na gwaji. To sai dai kuma, hakan na da nasaba da ci gaban yanayin da aka samu game da yaki da annoba, kana kuma za a yanke shawarar karshe, bayan dukkanin sassan masu ruwa da tsakin sun yi duba na tsanaki na watanni 3, gabanin zuwan lokacin gasar.