logo

HAUSA

Ya kamata a rika damawa da mata cikin harkokin shugabanci don cin gajiyar ilimi da basirarsu

2021-03-09 20:09:13 CRI

Ya kamata a rika damawa da mata cikin harkokin shugabanci don cin gajiyar ilimi da basirarsu_fororder_微信图片_20210309145517

Ranar 8 ga watan Maris, rana ce da MDD ta ware, a matsayin ranar mata ta duniya, da nufin jinjinawa rawar da mata ke takawa tare da kara fadakar da al’umma game da ’yanci da hakkokinsu.

Mata a ko ina sun kasance masu rauni, sai dai, irin rawa da gudunmawar da suke bayarwa wajen rayawa da kyautata al’umma a dukkan fannoni, ba zai misaltu ba.

Mata a fadin duniya sun cancanci samun ingantacciyar rayuwa ba tare da wariya ko kyama ko cin zarafi ba, mai kuma cike da daidaito da damarmaki iri daya da takwarorinsu maza. Idan kuma har ana son cimma wannan buri, to ya zama wajibi a rika damawa da su a dukkan harkokin rayuwa.

Taken ranar a bana shi ne “Mata a fannin shugabanci: cimma daidaito a duniya mai fama da COVID-19”. Wanda ke da nufin jinjinawa kokarin da mata da ’yan mata suka yi a fadin duniya, wajen tsara makoma mai cike da adalci da farfadowa daga annobar COVID-19 da kuma bayyana gibin da har yanzu ke akwai tsakaninsu da takwarorinsu maza.

Ya kamata a rika damawa da mata cikin harkokin shugabanci don cin gajiyar ilimi da basirarsu_fororder_微信图片_20210309145524

Rawar da mata ke takawa a dukkan fannonin rayuwa na ingiza ci gaba ga kowa. Sai dai, har yanzu ba sa samun wakilcin da ya dace a harkokin da suka shafi al’umma da tsara manufofi da shuagabnci. A cewar MDD, mata na shugabantar kasashe ko gwamnatoci 22, kuma kaso 24.9 cikin dari na ’yan majalisar dokokin ne kadai mata. Don haka, a irin wannan yanayi da ake ciki, za a dauki shekaru 130 nan gaba kafin a tabbatar da daidaito a fannin shugabanci tsakanin maza da mata.

Yayin da ake fama da annobar COVID-19, an ga yadda mata suka taka rawa a matsayin Likitoci da jami’an jinya da masu aiki gwaji, kuma masana kimiyya da dai sauransu. Sai dai, alkaluma sun nuna cewa, akwai bambancin kaso 11 cikin dari na albashinsu da takwarorinsu a fadin duniya. Baya ga haka, an ga yadda aka samu karuwar cin zarafinsu a wannan lokaci da suke bada gagarumar gudunmuwa wajen kare lafiyar al’umma.

Da yake jawabi domin ranar, zaunannen jakadan kasar Sin a MDD, Zhang Jun, ya tabbatar da irin rawar da mata suke takawa a kasar Sin, inda ya ce mata ne suka mamaye kaso 2 bisa 3 na jami’an lafiya da suka yi aikin tunkarar cutar COVID-19, haka kuma sun bada gagagrumar gudunmuwa ga nasarar kasar ta yaki da talauci. Lamarin da ya nuna cewa, ba gajiya kadai suka ci ba.

Ba a kasar Sin kadai ba, mata a ko ina suna taka muhimmiyar rawa ga ci gaban duniya. Sai dai duk da hakan, har yanzu da sauran rina a kaba wajen tabbatar da ’yanci da ba su kariya.

Ya kamata gwamnatoci da hukumomi da masu ruwa da tsaki, su rika sanya mata a kan gaba yayin da suke tsara manufofi don ba su dama da cin gajiyar ilimi da dabara da basirar da suke da ita, wadda ba makawa, za ta kara samar da ci gaban al’umma. (Fa’iza Mustapha)