logo

HAUSA

Halin karamcin da Sin ke nunawa Afrika zai cigaba kyautata alakar dake tsakanin bangarorin biyu

2021-03-08 18:13:40 CRI

Halin karamcin da Sin ke nunawa Afrika zai cigaba kyautata alakar dake tsakanin bangarorin biyu_fororder_38

Yayin da a makon jiya aka bude muhimman tarukan shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, mahukuntan kasar sun tabo batutuwa da dama dake da nasaba da batun cigaban kasar har ma da yadda kasar Sin za ta ci gaba da kyautata alakarta da sauran sassan duniya. Nahiyar Afrika wani muhimmin ginshiki ne a tsarin huldar Sin da kasashen duniya, musamman duba da yadda a koda yaushe kasar ke cigaba da kokarin neman kyautata mu’amalarta da kasashen na Afrika wacce ta dauke su a matsayin manyan aminanta. A cikin wani jawabin da ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ya bayyana a karshen wannan mako cewa a halin yanzu, taimakawa kasashen Afirka daban-daban wajen yaki da cutar COVID-19, gami da farfado da tattalin arzikinsu, batutuwa ne masu muhimmanci ga hadin-gwiwar Sin da Afirka. A wajen taron manema labarai na zama na hudu na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 13, Wang Yi ya nuna cewa, a bara, shugaba Xi Jinping ya jagoranci taron koli na musamman na hadin-gwiwar Sin da Afirka wajen dakile cutar COVID-19, inda ya sanar da wasu sabbin matakai na tallafawa Afirka. Kawo yanzu, kasar Sin ta turawa kasashen Afirka kayayyakin yaki da cutar cikin gaggawa har sau 120, gami da tura tawagogin kwararrun likitoci zuwa kasashen Afrika 15, tare kuma da samar da alluran riga-kafin cutar ga kasashe 35 na nahiyar har da ita kanta kungiyar tarayyar Afirka wato AU. Har wa yau, kasar Sin tana samar da taimako wajen aikin gina babbar hedkwatar cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa ta Afirka CDC, da gaggauta gudanar da hadin-gwiwa tsakanin wasu asibitocin Sin da Afirka 30. Minista Wang ya kara da cewa, a bara ne aka cika shekaru 20 da kafuwar dandalin hadin-gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC. Hadin-gwiwar Sin da Afirka ta zama abun koyi ga hadin-gwiwar da ake yi tsakanin kasashe masu tasowa. Kuma a shekarar da muke ciki, Sin da Afirka za su gudanar da sabon taron dandalin tattauna hadin-gwiwarsu a kasar Senegal, inda kasar Sin take sa ran amfani da wannan dama don marawa Afirka baya wajen ganin bayan cutar COVID-19, da gaggauta raya masana’antu, da kokarin dunkulewar nahiyar baki daya, da kuma taimaka mata wajen warware matsaloli bisa hanyar siyasa. Inganta hadin-gwiwar Sin da Afirka wajen raya shawarar “ziri daya da hanya daya”, da kara raya al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya tsakaninsu zai samar da sabon kuzari ga ci gaban nahiyar Afirka mai dorewa. (Ahmad Fagam)