logo

HAUSA

Shaidu sun karyata jita-jitar da ake yadawa game da alluran riga-kafin cutar COVID-19 na kasar Sin

2021-03-08 22:04:54 CRI

Shaidu sun karyata jita-jitar da ake yadawa game da alluran riga-kafin cutar COVID-19 na kasar Sin_fororder_1

Jiya Lahadi, mamban majalisar gudanarwa kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana a wajen taron manema labarai cewa, ko alluran riga-kafin cutar COVID-19 na kasar Sin ne, ko na wasu kasashe, idan har suna da nagarta da aminci, to za mu fada. Ya dace kasashen dake da karfi su yi bakin kokarinsu wajen samar da alluran ga al’ummomin kasashe daban-daban cikin farashi mai rahusa, ta yadda kowa da kowa zai iya cin gajiyarsu.

Shaidu sun karyata jita-jitar da ake yadawa game da alluran riga-kafin cutar COVID-19 na kasar Sin_fororder_2

Kalaman na minista Wang na zuwa ne, daidai da alkawarin da kasar Sin ta dauka tun farko, wato mayar da alluran riga-kafin a matsayin kayan amfanin kowa da kowa a duniya, al’amarin da ya shaida matukar kokarin da kasar Sin take yi, musamman a matsayinta na kasa dake sauke nauyin dake wuyanta.

A gaskiya, kasar Sin tana bakin kokarinta wajen cika alkawarin da ta yiwa duniya baki daya. Tun da farko, kasar Sin ta yi gwajin wasu nau’o’in alluran riga-kafin cutar 17 a kan wasu mutane, kuma sama da kasashe 60 sun bada izinin amfani da su. Daga baya kuma, ta samar da tallafin alluran ga kasashe masu tasowa 69 wadanda ke da matukar bukata, da fitar da su zuwa kasashe 43. Har wa yau, kasar Sin ta ba wa sojojin dake aikin tabbatar da zaman lafiya na kasa da kasa alluran riga-kafin kyauta, da samar da su ga ‘yan wasannin motsa jiki wadanda za su halarci gasar Olympics.

Shaidu sun karyata jita-jitar da ake yadawa game da alluran riga-kafin cutar COVID-19 na kasar Sin_fororder_3

Abu mafi muhimmanci shi ne, kasar Sin ta fitar gami da samar da tallafin alluran riga-kafin ba tare da neman cimma wasu muradu ko kuma gindaya wani sharadin siyasa ba, tana yi ne don nuna jin kai.

Amma duk da haka, kokarin da kasar Sin ko wasu kasashe kalilan suke yi na dakile yaduwar cutar bai isa ba. Ana fatan dukkan kasashen dake da karfi, za su iya samar da alluran riga-kafin cutar ga kasashen dake da bukata, musamman kasashe masu tasowa, a kokarin taimakawa duk duniya ganin bayan cutar.(Murtala Zhang)